An Gano Hatsabibin Kwamandan Turji, an Faɗi Hatsarin 'Duna Sani' da Sheɗancinsa

An Gano Hatsabibin Kwamandan Turji, an Faɗi Hatsarin 'Duna Sani' da Sheɗancinsa

  • Wani matashi da aka ga a hotonsa yana rike da bindiga an bayyana shi a matsayin “Duna Sani,” babban kwamandan Bello Turji
  • Ana zargin Duna Sani da kisan mutane da dama, yanke kawunan mata da cin zarafin Bayin Allah da sauran munanan laifuffuka
  • Turji ya yi ikirarin cewa Duna Sani ba zai shafe kwanaki uku ba tare da ya kashe wani mutum ba, lamarin da ya ta da hankula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zamfara - Hatsabibin ɗan bindiga, Bello Turji ya bayyana wani kwamandansa na musamman a hoto.

Wani mutum da aka hango a hoto da ya yadu sosai yana rike da bindiga, an bayyana shi a matsayin 'Duna Sani'.

Wani kwamandan Bello Turji ya bayyana
Bello Turji ya fadi hatsarin Duna Sani a cikin rundunarsa. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Source: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ya ce Duna na daga cikin manyan kwamandojin fitaccen dan bindiga, Bello Turji.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Yadda dan sanda ya tsere da gudu bayan kama kwamishinansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake kokarin tattaunawa da Bello Turji

Wannan bayanan na fito wa ne bayan Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tabbatar da cewa sun tattauna da Turji a dajin jihar Zamfara.

Malamin ya ce sanadin tattaunawar ta su har dan bindigan ya saki wasu daga cikin mutanen da ya yi garkuwa da su da kuma ajiye wasu makamai.

Sai dai kuma maganganun malamin sun bar baya da kura yayin da wasu ke kushe maganar sulhu saboda yawan al'umma da ke rasa rayukansu kan ta'addanci a kullum.

Turji: An kalubalanci Sheikh Asadus Sunnah

Daga cikin waɗanda ke kalubalantar matakin har da takwarorinsa malaman Musulunci da suke ganin hakan kuskure ne.

A martaninsa, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi watsi da ra'ayin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa Musulunci ya umurci a yake su.

Malamin ya bayyana cewa addini da dokar kasa duk sun amince a kashe su ko a hukunta su matukar suna ci gaba da barna.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi maganar halin da ake ciki, ya ɗauko tarihin sama da shekaru 10

Ya kalubalanci masu cewa ‘yan bindiga sun fi karfin jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati na da ikon kawo karshen su.

Bello Turji ya fadi hatsarin Sani Duna a rundunarsa
Ana zargin wani kwamandan Turji da kisan kiyashi a Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Hatsarin kwamandan Turji da ake kira 'Duna Sani'

Ana bayyana Duna Sani a matsayin daya daga cikin mafi hatsari a rundunar Turji wanda kuma yana ji da shi.

Ana zarginsa da kashe mutane marasa adadi, yanke kan mata, da aikata munanan laifuffukan cin zarafin mata a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Turji da kansa ya ce a cikin wani faifan sauti cewa Duna Sani ba zai iya shafe kwanaki uku ba tare da ya kashe wani mutum ba.

Ana ta kiraye-kiraye, inda mutane da dama ke bukatar a kawo karshen Duna Sani, Bello Turji, da makamantansu da suka dade suna addabar al’umma a yankin.

An soki maganar tattaunawa da Bello Turji

Mun ba ku labarin cewa sakin mutane 32 da Bello Turji ya yi ya janyo maganganu, yayin da wasu ke ganin hakan tamkar dawowa da tsohon kuskure ne..

Alhaji Sani Shinkafi ya ce tattaunawar da aka yi da Turji ba ta da amfani, inda ya bayyana ta a matsayin rashin adalci.

Hakan ya biyo bayan kokarin Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah da ya ce sun tattauna da dan ta'addan lokuta da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.