Sakkwato: Garuruwa Sun Zama Kufai, 'Yan Ta'adda Sun Raba Dubunnan Mutane da Gidajensu
- Hare-haren ‘yan bindiga sun tilasta wa dubunnan mazauna Tureta da Dange/Shuni barin gidajensu, yayin da ƙauyuka da makarantu suka zama kufai
- ‘Yan gudun hijira na fama da yunwa, rashin ruwa da magani, inda yara ke shan matsananciyar wahala da dakatar da karatu
- Shugabannin yankin sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro su ɗauki matakin gaggawa tare da tura sojoji na dindindin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Tureta da Dange/Shuni, ƙananan hukumomi biyu a jihar Sokoto, na cikin wani mummunan hali sakamakon rikicin tsaro da na jin kai da ke ƙara tsananta.
Hare-haren ‘yan bindiga sun tilasta wa dubban mazauna – mafi yawansu mata da yara – barin gidajensu, suna tsugunne a ƙarƙashin bishiyoyi ko cikin daji ba tare da mafaka mai kyau ba.

Kara karanta wannan
Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Source: Original
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, tsofaffin ƙauyukan noma masu zaman lafiya yanzu sun koma ƙauyuka marasa mutane, bayan tserewar mazauna saboda tsoro da maimaita hare-hare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna na barin gidajensu, makarantu na rufewa
Vanguard ta ruwaito cewa, sakamakon ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, ƙauyuka da dama sun zama kufai, yayin da makarantu suka daina aiki.
Wata mazauniyar yankin, Malama Halima Denge, ta bayyana yadda rashin tsaro ya yi wa rayuwarsu katutu.
Ta ce:
“Wata uku kenan ban shiga gidana ba,” in ji Halima, uwa ‘yar gudun hijira mai yara huɗu daga Tureta.
“Kullum muna kwana a waje, ba don muna so ba, sai don muna ganin mun fi samun tsaro a daji fiye da gidajenmu.”
Mazauna sun bayyana cewa aƙalla ƙauyuka 12 a cikin waɗannan ƙananan hukumomi biyu an kai musu hare-hare sau da dama, inda ‘yan bindiga ke sace shanu, yin garkuwa da mutane, da fasa gidaje.
Ya ce:

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Gwamnatin Tarayya ta kori ma'aikata, ta tilasta wa wasu ajiye aiki a Najeriya
“Yanzu gonakinmu sun lalace, dabbobinmu sun ƙare, muna rayuwa cikin tsantsar tsoro.”
Al'ummar Sakkwato na cikin yunwa
Mutanen da aka raba da muhallansu na fama da matsananciyar ƙuncin rayuwa saboda babu abinci, babu ruwan sha mai tsafta, babu kuma magani.
Wasu sun ce suna zama ne a sansanonin wucin gadi ko kuma ƙarƙashin bishiyoyi, da tarkacen zane kawai ke rufe su.

Source: Facebook
Yara na cikin mawuyacin hali musamman, inda karatu ya tsaya cak, kuma damuwar zuciya ke ƙaruwa a kullum.
Wani jagoran matasa a yankin ya bayyana takaici kan yadda ya ce martanin hukumomi ke tafiya a hankali kuma ba ya tasiri.
Ya ce:
“Kusan kowace rana ana kai hare-hare. ‘Yan bindiga suna aiki ba tsoro ba – ma har a rana tsaka. Mutane sun fara rasa imani da ikon gwamnati na kare su."
Wani mazaunin Lambar Tureta, wanda ya roƙi a sakaya sunansa, ya ce duk da cewa jami’an tsaro na ƙoƙarin yin aiki, amma matakan ba su isa ba.
Yan ta'adda sun zubar da makamai
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda sun mika wuya tare da tuba daga miyagun ayyukan daukar rayukan jama'a ba gaira babu dalili.
Ta ƙara da cewa sama da ‘yan ta’adda 300 da suka tuba na halartar wani shirin gyara halayya, kuma ana koya masu sana'o;i domin a shirya mayar da su cikin al’umma.
Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo-Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja a taron masu ruwa da tsaki kan gyara halayyar 'yan ta'addan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
