Kanawa na cikin Alheri, Tinubu zai Musu Jirgin Kasa na Naira Tiriliyan 1.5
- Gwamnatin tarayya za ta gina titin jirgin kasa a Kano wanda zai rage cunkoson abubuwan hawa a birnin
- Rahotanni sun bayyana cewa Hon. Abubakar Kabir Bichi ya ce aikin zai ƙara daraja ga tattalin arzikin jihar Kano
- Bichi ya ce shirin yana cikin muhimman ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar a Arewacin Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta gina layin dogo a cikin birnin Kano, wanda zai ci kuɗi Naira tiriliyan 1.5.
Wannan jawabi ya fito daga shugaban kwamitin kasafi na majalisar wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kano.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na jajircewar shugaban ƙasa Bola Tinubu wajen inganta abubuwan more rayuwa da bunkasa Arewa baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a gina titin jirgin kasan N1.5tr Kano
Hon. Kabir Bichi ya bayyana cewa aikin layin dogon zai ƙunshi kuɗi har Dala biliyan 1, wanda daidai yake da Naira tiriliyan 1.5.
Rahoton Trust Radio ya nuna cewa ya ce:
“Wadanda suka je kasashen waje musamman Turai da Asiya sun shaida irin amfanin irin wannan aiki. Wannan aiki zai ƙara darajar tattalin arzikin Kano.”
Ya ce aikin zai taimaka wajen magance cunkoso da wahalhalun sufuri a Kano, da samar da sauƙin zirga-zirga ga al’umma.
Tinubu na aiwatar da ayyuka a Arewa
Bichi ya musanta rade-radin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu bai damu da yankin Arewa ba, yana mai cewa:
“Ni shugaban kwamitin kasafi ne, kuma na san irin abubuwan da shugaban ya aikata domin ci gaban Arewa.”
Ya ce akwai ayyuka masu yawa da shugaban ƙasa ya kaddamar da su a bangaren lafiya, noma, ilimi, tsaro da abubuwan more rayuwa a yankin Arewa.

Kara karanta wannan
Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas
Ya bayyana cewa:
“A bangaren gina hanyoyi, aikin Kaduna-Zaria-Kano yana dab da kammaluwa.
Shugaban ya soke kwangilar hanyar Kaduna-Abuja kuma ya ba wani sabon kamfani, wanda har ya fara aiki.”

Source: UGC
Manyan ayyuka da aka kammala a Arewa
Hon. Bichi ya ƙara da cewa an riga an kammala aikin hanyar Kano zuwa Hadejia mai nisan kilomita 200.
Ya ce sannan an yi aikin hanyar Kano ta Arewa, wanda gwamnatin tarayya ta kashe sama da Naira biliyan 250 a kansa.
Bichi ya bayyana cewa zuwansu Kano ya danganci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC domin tsara dabarun tunkarar zaɓen 2027.
Ya ce taron ya kuma nuni da goyon bayan da suke bai wa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa rawar da ya taka wajen samun nasarorin jam’iyyarsu.
Sheikh Khalil zai yi takara a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa zai yi takarar gwamna a 2027.
Malamin ya bayyana cewa zai yi takarar ne a karkashin jam'iyyar ADC da ake kokarin kafa hadaka a cikinta.
Ya bayyana cewa yana maraba da shigar manyan 'yan adawa kamar Atiku Abubakar zuwa ADC domin tunkarar APC a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

