Ana Batun Sulhu da Turji, Gwamna Bago Ya Fadi Matsayarsa kan Tattaunawa da 'Yan Bindiga

Ana Batun Sulhu da Turji, Gwamna Bago Ya Fadi Matsayarsa kan Tattaunawa da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya koka kan matsalar ayyukan 'yan bindiga da ake fama da ita a jiharsa
  • Umaru Bago ya bayyana cewa sulhun da ake yi da 'yan bindiga a wasu jihohin ne ya sanya suke kwararowa zuwa jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa ba zai taba shiga cikin kowace irin tattaunawa da bindiga ba wadanda suke farmakar bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi magana kan matsalar ayyukan 'yan bindiga a jiharsa.

Gwamna Bago ya bayyana cewa shirin yin sulhu da ‘yan bindiga da wasu jihohi makwabta ke yi ne ya jawo karuwar zuwan su cikin jihar Neja.

Gwamna Bago ya koka kan 'yan bindig
Gwamna Bago ya ce sulhu na sa 'yan bindiga kwarorowa Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce Gwamna Umaru Bago ya bayyana hakan ne a wajen taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki game da aiwatar da dokar kula da zirga-zirgar dabbobi da samun takardar izinin duba lafiyar dabbobi da aka gudanar a birnin Minna.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bello Turji ya saki sabon bidiyo kan sulhu, ya kira babban malami da 'ɓarawo'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Bago ya ce kan sulhu da 'yan bindiga?

Da yake nuna damuwarsa game da karuwar masu satar shanu da ‘yan bindiga a jihar, Gwamna Bago ya ce ba zai taɓa shiga kowace irin tattaunawa da su ba.

Ya kara da cewa sulhun da wasu jihohi ke yi da ‘yan bindiga ya sa aka samu karin satar shanu, lamarin da ya bayyana a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Saboda haka, Gwamna Bago ya ce za a nemi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro su shiga tsakani domin magance matsalar.

Game da batun shigo da naman dabbobi da aka yanka daga daji domin sayarwa, gwamnan ya ce za a ɗauki matakai ta hannun hukumomin da suka dace don tabbatar da cewa naman da ake sayarwa ya fito ne daga wuraren yanka da aka amince da su kawai.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Ya ƙara da cewa duk wasu dabbobi da za a shigo da su cikin jihar dole ne a yi musu rigakafin cututtuka kafin a shiga da su.

Gwamna Bago ya ba da umarni kan noma

Haka kuma, ya bayar da umarni cewa babu wani aikin noma da za a gudanar a gefen hanya, sannan ya gargadi makiyaya da kada su bar dabbobinsu su ci gonakin mutane, inda ya ce duk wanda aka kama da laifi za a hukunta shi.

Gwamnan ya ce dokar kula da cututtukan dabbobi ta 2022, sashe na 18 da 19, ta ba da iko ga ma’aikatar kula da lafiyar dabbobi a jihar su ba da takardar izinin safarar dabbobi, kaji da kayayyakin dabbobi.

Ya jaddada cewa wannan mataki zai inganta lafiyar jama’a, gyara tsarin kasuwanci, da kuma kare rayuwar jama’a da hanyoyin samun abinci.

'Yan bindiga sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi wa dakarun sojoji kwanton bauna a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun yi wa sojojin kwanton bauna ne bayan motar da suke ciki ta lalace a tsakiyar daji.

Harin kwanton baunan ya jawo an hallaka soja guda daya tare da raunata wasu bayan sun bude musu wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng