Abba Ya Yi Magana a Fusace bayan 'Yan Daban Kano Sun Yi Ajalin Hadiminsa

Abba Ya Yi Magana a Fusace bayan 'Yan Daban Kano Sun Yi Ajalin Hadiminsa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai wa Sadiq Gentle da ya yi sanadiyyarsa
  • Ya ce marigayin ya kasance mai kishin kasa da jajircewa a aikinsa na yada labarai a ma'aikatar tarihi da al’adu
  • Gwamnan ya umurci hukumomin tsaro su kama wadanda suka aikata kisan cikin gaggawa domin girbar abin da suka shuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar jami’in yada labarai da ke aiki a ma’aikatar tarihi da al’adu ta jihar, Sadiq Gentle.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargi da aikata ta’addanci ne suka kai masa hari da ya jikkata shi, kafin daga bisani ya rasu.

Abba Kabir Yusuf ya bukaci kama wadanda suka kai wa Sadiq Gentle hari
Abba Kabir Yusuf ya bukaci kama wadanda suka kai wa Sadiq Gentle hari. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook, an bayyana mamacin a matsayin jarumi kuma mai kishin kasa a harkar kafafen sadarwar zamani.

Kara karanta wannan

An kashe mai yi wa dakin Ka'aba hidima da makami mai kaifi a Birtaniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Abba kan rasuwar Sadiq Gentle

Gwamna Abba ya ce mutuwar Malam Sadiq Gentle ta girgiza shi kwarai da gaske, domin kuwa ya kasance mutum mai kamun kai da da aiki tukuru.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai zaman lafiya da gaskiya, wanda ya sadaukar da kansa ga ci gaban jihar Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta ce kisan da aka yi masa keta mutuncin bil’adama ne da ba za a lamunta ba.

Lokacin da Sanusi II ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti
Lokacin da Sanusi II ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Abba Kabir ya yi tir da yi wa Sadiq rauni

A cikin jawabin nasa, Gwamnan ya yi tir da harin da aka kai wa Sadiq Gentle da ya kira da ta’asa da aikin dabbanci.

Ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci irin wannan danyen aiki ba, inda ya bukaci daukar matakin gaggawa.

Umurnin kama wadanda suka aikata laifin

Gwamna Abba ya umarci hukumomin tsaro da su yi cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aikar.

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

Ya bukace su da su tabbatar da cewa wadanda suka aikata kisan sun fuskanci hukunci daidai da doka.

Bugu da ƙari, ya jajanta wa iyalan marigayin da abokan aikinsa da sauran ma’aikata, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na tare da su a wannan lokaci na jimami.

An yi wa Sadiq Gentle jana'iza a Kano

Fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta nuna alhini kan harin da aka kai wa matashin da ya yi sanadiyar kawo karshen rayuwar shi.

Masarautar ta wallafa a X cewa an gudanar da sallar jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana, a Kofar Kudu, Gidan Sarki.

Sarki Sanusi II ya ziyarci Sadiq Gentle

A wani rahoton, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti bayan harin da aka kai masa.

A lokacin da Khalifa Muhammadu Sanusi ya ziyarci Sadiq, ya same shi cikin mummunan yanayi tare da masa addu'a.

Kafin zuwan mai martaban duba shi a asibitin Murtala, Legit Hausa ta gano cewa Sarkin Yakin Kano ya je asibitin duba lafiyar matashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng