'Yan Daba Sun Yi wa Masoyin Sanusi II Ta'addanci a Kano, Sarki Ya Tafi Asibiti

'Yan Daba Sun Yi wa Masoyin Sanusi II Ta'addanci a Kano, Sarki Ya Tafi Asibiti

  • Mai martaba Sarki, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya ziyarci Sadiq Gentle da aka kai wa hari a jihar Kano
  • Wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Sarkin Yakin Kano ta soma kai masa ziyara domin jajanta masa da yi masa addu'a
  • An kai wa Gentle hari da dare inda aka ji masa raunuka masu tsanani a jikinsa kuma har yanzu yana kwance a asibiti

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mai martaba Sarki Khalifa Muhammad Sanusi II, ya kai ziyarar jaje domin duba lafiyar wani matashi da ke daya daga cikin magoya bayansa mai suna Sadiq Gentle.

Rahotanni sun nuna cewa wasu bata-gari ne suka kai wa matashin hari kuma ya samu raunuka masu tsanani.

Sarki Sanui II ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti
Sarki Sanusi II ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti. Masarautar Kano
Source: Facebook

A bidiyon da masarautar Kano ta wallafa a X, Legit Hausa ta hango Sarkin na yi wa Sadiq Gentle addu'a a cikin asibiti.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Sarkin Kofa ya dawo bangaren Sanusi II, ya yi watsi da Aminu Ado

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya kai ziyarar ne asibitin Murtala da ke cikin birnin Kano, inda aka kwantar da matashin bayan jin rauni a jikin sa sakamakon hari da aka kai masa.

Sarkin Yaki ya wakilci Sanusi II

A farko, mai girma Sarkin Yakin Kano ya jagoranci tawaga zuwa asibitin, inda ya isar da sakon mai martaba ga iyalan Sadiq Gentle da ke cikin damuwa sakamakon wannan hari.

A cewarsa, Masarautar Kano za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an taimaka wa matashin da kulawa.

An ce wannan ziyara ta nuna yadda Masarautar ke ƙaunar jama’arta, tare da kula da lafiyar wadanda ke goyon bayanta cikin al’umma baki ɗaya.

Sarkin Yakin Kano ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti. Hoto: Khalifa Muhammad Sanusi ll fans
Sarkin Yakin Kano ya ziyarci Sadiq Gentle a asibiti. Hoto: Khalifa Muhammad Sanusi ll fans
Source: Facebook

Ziyarar Sarkin Yakin ta kasance a matakin farko kafin Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya samu damar zuwa da kan shi.

Muhammadu Sanusi II ya ziyarci Sadiq a asibiti

Bayan zuwan Sarkin Yaki, Mai martaba da kansa ya kai ziyarar duba lafiyar Sadiq Gentle a ranar Litinin, 4 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Bayan barin kujerar APC, Hadimin Ganduje ya zargi Gwamnatin Tinubu da son kai

Sarkin ya ga irin raunin da aka ji wa matashin, ciki har da caka masa wuƙa a wasu sassan jikinsa.

Sarkin ya roƙi Allah ya ba matashin lafiya tare da yin addu’ar Allah ya tona asirin masu wannan ta’addancin.

Ana ganin ziyara za ta ƙara bai wa iyalan matashin ƙarfin guiwa da fatan samun mafita da taimako daga Masarautar.

Rikicin daba ya yi kamari a jihar Kano

Wannan hari ya faru ne a daidai lokacin da jihar Kano ke fama da karuwar ayyukan 'yan daba a sassanta.

Lamarin ya sa rundunar ‘yan sanda ta ƙaddamar da shirin “Operation Kukan Kura” domin fatattakar miyagu a fadin jihar, kamar yadda SP Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

Rahotanni sun nuna cewa masu irin wannan hari na fakewa da duhun dare suna ta’addanci a cikin gidajen jama’a da wasu wurare, inda suke barazana ga rayuwar al’umma.

Sarkin Kofa ya nemi gafarar Sanusi II

A wani rahoton, kun ji cewa Balarabe Sarkin Kofa ya nemi gafarar mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Musulmi sun fusata da dodanni suka farmaki limamin Musulunci, an roki gwamna

Hakan na zuwa ne bayan Sarkin Kofa ya janye goyon bayan shi ga bangaren fadar Nasarawa zuwa Gidan Rumfa.

Balarabe Sarkin Kofa ya gurfana a fadar Sanusi II a ranar Litinin, 7 ga Agusta, 2025 domin jaddada yi masa mubaya'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng