An Tara Gima Giman Malamai a Kaduna, Sun Bada Fatawa kan Tazarar Haihuwa a Musulunci

An Tara Gima Giman Malamai a Kaduna, Sun Bada Fatawa kan Tazarar Haihuwa a Musulunci

  • Manyan malamai a Kaduna sun bayyana cewa ya halatta ma'aurata su bayar da tazarar haihuwar yara domin kula da lafiyar mata
  • Sun bayyana hakan ne a wurin wani taron kwana ɗaya da ƙungiyar DKT Nigeria International ta shirya a Kaduna
  • A cewar malaman, Musulunci ya koyar da ba da tazarar haihuwa saboda lafiyar yara da mata, suka kafa hujjoji da ayoyi da Hadisai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Manyan Malaman Addinin Musulunci a Jihar Kaduna sun bayar da fatawar cewa ya halatta ma'aurata su rika bada tazara tsakanin haihuwar yara.

A cewar malaman, addinin Musulunci ya amince da hakan tare da bayyana amfaninsa ga lafiyar mata da yara.

Malamai sun ce bada tazarar haihuwa ya halatta.
Malaman Musulunci a Kaduna sun ba da fatawa kan tazarar haihuwa Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ce an bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai na yini daya da aka shiryawa malamai da limamai, wanda ƙungiyar DKT Nigeria International ta dauki nauyi.

Kara karanta wannan

Babu dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata yayin wani hari a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya duba koyarwar addinin musulunci da ilimin lafiya kan batun tazarar haihuwa ta hanyar tattaunawa da manyan malamai masu tasiri a cikin al’umma.

Malaman Kaduna sun yarda da tazarar haihuwa

A lokacin da yake jawabi a taron, Dr. Yakubu Arrigasiyyu, malami daga Majalisar Malamai ya jaddada cewa Musulunci bai haramta bayar da tazarar haihuwa ba.

“Mun yi bincike da nazari game da batun tazara tsakanin haihuwa, musamman daga mahangar addinin Musulunci.
"Akwai Hadisai da ayoyin Alkur’ani da ke nuna yadda Musulunci ke goyon bayan iyaye wajen tsara lokacin da suka dace su haifi yara.”

- Dr. Yakubu Arrigasiyyu.

Gudummuwar da ya kamata malami su bayar

Ya kara da cewa malamai suna taka rawar gani wajen fahimtar da al'umma da koyar da su ilimin da ya kamata su sani dangane da lafiyarsu.

"Malaman Musulunci shugabanni ne, su ne ke jagorantar mutane kuma su koya musu abin da ya dace da abin da bai dace ba.

Kara karanta wannan

Amnesty Int'l ta dura kan Tinubu da gwamnati ta ƙi tsoma baki shekaru 6 da 'sace' Dadiyata

"Idan suka fahimci alherin abu da abinda ya dace, to su ma za su iya yada wannan ilimi zuwa ga mabiyansu," inji shi.

Dr. Yakubu ya roki malamai su isar da wannan saƙo mai muhimmanci game da bada tazarar haihuwa domin kula da lafiyar yara da mata.

Dalilin da ya sa DKT ta shirya taron

A nata bangaren, Husseina Dada, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar DKT Nigeria International, ta ce sun zaɓi ganawa da malamai ne saboda yadda al'umma suka yarda da su.

"Mu fahimci cewa malamai ya kamata mu fara tattaunawa da su kan batun tazarar haihuwa. Ba da tazara tsakanin yara abu ne mai matukar muhimmanci ga kowace matar aure.
"Mahaifa tana bukatar hutu. Wannan yana ba mata damar farfadowa da kuma ciyar da jaririnsu da abinci mai gina jiki.”

Ta kara da cewa tsarin tazara yana bai wa mata damar kula da gida, sana’a da lafiyarsu yadda ya kamata.

Sarkin Musulmi ya halarci taro a Ingila

A wani rahoton, kun ji cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya halarci taron shugabannin Musulmi na duniya a Oxford da ke ƙasar Ingila.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin ministan Tinubu da Gwamna, an ci gyaran Bago kan matakinsa

Sultan ya bukaci shugabanni da al’umma su rungumi zaman lafiya a matsayin hanyar samun hadin kai da zaman lafiya a duniya.

Ya ƙara da cewa addinin Musulunci na koyar da zaman lafiya, don haka ya kamata a ci gaba da amfani da koyarwar Musulunci wajen tabbatar da fahimtar juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262