Jami'an 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Bindiga yayin Arangama a Zamfara
- Jami'an 'yan sanda sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga yayin wani artabu da suka yi a jihar Zamfara
- Tawagar 'yan sandan wacce take tare da 'yan sa-kai sun yi arangama da 'yan bindigan ne a kauyen Fegin Kanawa na hukumar Gusau
- An dai yi musayar wuta ne lokacin da jami'an tsaron ke shirin kai agajin gaggawa bayan samun rahoton shirin 'yan bindiga na kai hari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Jami'an ‘yan sanda a jihar Zamfara sun harbe wasu ‘yan bindiga takwas har lahira yayin wata musayar wuta da suka yi.
Jami'an 'yan sandan sun harbe tsagerun ne a kauyen Fegin Kanawa da ke yankin Wonaka a karamar hukumar Gusau, bayan wani kwanton-bauna da 'yan bindigan suka shirya.

Source: Twitter
'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton da kwamandan rundunar (Zonal Force Squad - ZFS) ya bayar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 4:30 na yamma.
Lamarin ya auku ne lokacin da wata tawagar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da ‘yan sa-kai daga kauyen Fegin Mahe suka samu bayanan sirri kan wani yunkurin harin ‘yan bindiga da ake shirin kai wa.
Ba tare da sanin jami’an tsaron ba, ‘yan bindigan sun riga sun tare hanya tare da yin kwanton-bauna, inda suka bude wuta a kan tawagar yayin da suke kusantar wurin da suke son zuwa.
Sai dai jami’an sun mayar da martani da karfin wuta fiye da na ‘yan bindigan, lamarin da ya kai ga hallaka ‘yan bindiga takwas, yayin da wasu da dama suka tsere cikin daji da yiwuwar samun raunukan harbin bindiga.
A yayin musayar wutar, wani jami'in dan sanda mai suna Insfekta Tasi'u Lawali daga rundunar ‘38 Mobile Force (PMF) Gusau ya samu raunin harbin bindiga a hannunsa da bakinsa.
An garzaya da shi zuwa asibitin tarayya (FMC) da ke Gusau domin samun kulawar gaggawa, kuma rahotanni sun ce yana cikin yanayi mai kyau.
Rundunar ‘yan sanda ta kara kaimi wajen gudanar da bincike da sintiri a dazukan da ke kewaye domin nemo sauran ‘yan bindigar da suka tsere.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan sanda
- Damfara: Rundunar ƴan sanda ta kama matashi da ke kwaikwayon muryar gwamnoni
- Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda 2 da ke tsaron wani ɗan majalisa
- Fitinannen uban daba a Kano, Barga ya faɗa komar ƴan sanda
'Yan sanda sun gwabza da 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Katsina, sun yi gumurzu da wasu 'yan ta'adda.
'Yan sandan sun samu nasarar dakile yunkurin da miyagun suka yi har sau biyu na sace mutane a karamar hukumar Sabuwa.
A yayin artabun da aka yi, jami'an 'yan sanda sun samu nasarar kubutar da mutane 28 da aka yi yunkurin sace su.
Asali: Legit.ng

