Gwamnati Ta Aika Saƙo ga Masoyin Abba da zai Kawo Ziyara Kano a Ƙafa
- Gwamnatin Kano ta dakatar da shirin masoyin gwamnan Abba Kabir Yusuf da ke son tattaki daga Jigawa zuwa jihar
- Sanarwar gwamnatin Kano ta bukaci Lawan Habib ya koma gida domin rayuwarsa ta fi komai muhimmanci
- Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya fitar da sanarwa a kan batun ya ce addu'a za ta fi wa gwamnan amfani
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana samun labari kan wani bawan Allah da ke matuƙar ƙaunar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Rahotanni da suka iske Darakta Janar na Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature D-Tofa, na cewa mutumin mai suna Lawan Habib ɗan asalin jihar Jigawa ne.

Source: Facebook
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce yanzu haka Malam Lawan na shirin yin tattaki daga Jigawa zuwa Kano domin ganin gwamna.
Sakon gwamnan Kano ga masoyin Abba
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce ta ji daɗin irin soyayyar da Lawan Habib ya nuna wa gwamnan.
Sai dai ta ce bai kamata ya jefa kansa cikin haɗari ba da sunan zuwa Kano daga Jigawa a ƙafa.

Source: Facebook
Sanusi Bature D-Tofa ya ce:
"Mun samu labari wani bawan Allah mai suna Lawan Habib da ya taso daga Dutse na jihar Jigawa da niyyar zuwa Kano a ƙafa domin kai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ziyara.
"Muna kira gare shi ko duk wanda ya san shi da cewa don Allah ya koma gida cikin iyalansa. Babu buƙatar ya sa kansa cikin haɗari da wahala ba tare da dalili ba."
Gwamnati ta bayyana abin da Abba ke buƙata
A cewar Sanusi Bature, a yanzu ba wani abu da gwamnan Kano ke buƙata kamar addu’a domin tafiyar da jihar.
A kalamansa:
"Maigirma Gwamna ya gode da kauna, amma babban abin da muke buƙata shi ne, ya yi wa Gwamnan addu’a ta samun damar ci gaba da ayyukan da ya sa a gaba na hidimtawa al’ummar Kano. Mun gode."

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano
Tuni dai jama'a suka bayyana ra’ayoyinsu kan shirin masoyin gwamnan da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka.
Ra’ayoyin jama’a a shafin Facebook
Abubakar Yaro Mainasara ya ce:
"Gaskiya na ji daɗin wannan sanarwar. Har ga Allah na tsani masu irin wannan ɗabi’a marar manufa."
Aminatu Isma’il Adam ta ce:
"Ku bar shi kawai ya zo, daga Dutse zuwa Kano ai ba fiye da motsa jiki ba."
Nura Abdullahi Ahmad ya ce:
"To, zai iya hawa mota ya zo tun da an hana shi zuwa a ƙafa?"
Usamatu Sani Kofar Naisa ya ce:
"Saboda tsananin rowa ba za ku iya ba shi na mota ya taho don ya kawo muku ziyara ba? Allah ya raba mu da rowa."
Salim Abdullahi ya ce:
"Allah ya saka da alheri. Wannan kauna da goyon bayan da Lawan Habib ya nuna abin a yaba ne, amma lafiyarsa tafi muhimmanci. Allah ya kai shi gida lafiya, kuma ya karɓi addu’arsa ga Gwamna."
Gwamnatin Kano ta waiwayi bangaren lafiya
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta bayyana shirin gyara cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a faɗin jihar.
A cewar sanarwar da Ibrahim Adam, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, gwamnatin za ta gyara sibitoci 203 a cikin faɗin Kano.
Gwamnatin ta ce kowace karamar hukuma za ta amfana da sabuwar cibiya mai inganci da kayan aiki na zamani domin inganta rayuwar mazauna karkara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

