Yadda Aka Samu kusan Naira Tiriliyan 1 da Za a Gyara Filin Jirgin Saman Legas
- Gwamnatin Tarayya za ta gina sabon sashe na filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos da kuɗi har N712bn
- Ministan jiragen sama, Festus Keyamo ya ce za a biya kuɗin ne daga rarar da aka samu bayan cire tallafin mai da sauya tsarin canjin kuɗi
- Ya ce filin jirgin na yanzu ya lalace ƙwarai kuma hakan na barazana ga jiragen ƙasashen waje da ke sauka a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ce za ta yi amfani da Naira biliyan 712 da ta samu daga cire tallafin man fetur wajen gina sabon sashe na filin jirgin Murtala Muhammed da ke Lagos.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce sabunta filin jirgin na da matuƙar muhimmanci domin daidaita Najeriya da ƙasashen da ke da ingantattun filayen jiragen sama.

Kara karanta wannan
Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Source: Facebook
Keyamo ya bayyana haka ne yayin wata hira ta musamman da aka yi da shi a Channels TV ranar Lahadi.
Keyamo ya kare gyaran filin jirgin N712bn
Yayin kare matakin gwamnatin Bola Tinubu na kashe makudan kudi wajen gyara filin jirgin Legas, Keyamo ya bayyana cewa:
“Rufin filin jirgin na fitar da ruwa. Ginin ya lalace, wari na fita, kana iya ganin wasu na sayar da Indomie a ciki.”
Ya ce kayan aiki da yawa a filin jirgin sun daina aiki saboda babu kayan gyara a kasuwa, kuma hakan yana cutar da tsaro da aikin kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje.
Za a yi aiki da kudin tallafi a Legas
Yayin da gwamnati ke kare matakin, wasu ‘yan Najeriya na ganin cewa kashe kudi a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa da yunwa a ƙasar bai dace ba.
Sai dai Ministan ya ce wannan aiki yana daga cikin alkawurran da gwamnatin Tinubu ta dauka na yin manyan ayyukan more rayuwa da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin mai.
The Cable ta rahoto cewa gwamnati na fatan wannan sabon gini zai mayar da Lagos babbar cibiyar sufurin jirage a yammacin Afirka.
Za a gina sabon sashen filin jirgi
Ministan ya ƙara da cewa aikin ba wai zai tsaya a kwaskwarima ba ne kawai, za a rusa sashen ne gaba ɗaya sannan a sake gina shi daga tushe.
“Za mu rushe wani sashen shi gaba ɗaya, mu bar ginshiƙai kawai. Za a zana sabon tsarin da zai dace da na zamani.”
Ya ce aikin zai ɗauki wata 22 kafin a kammala, kuma burin gwamnati shi ne ta gina wani katafaren filin jirgi da zai iya gogayya da na kasashen Afirka irin su Habasha da Afrika ta Kudu.

Source: Getty Images
Filin jirgin zai bunƙasa sufuri da tattali
Festus Keyamo ya ce babu yadda za a cigaba da tafiyar da filin jirgin Lagos kamar yadda yake yanzu.
Ya ce barin filin jirgin saman a haka yana hana Najeriya samun damar haɓaka a harkar sufurin jirage.
“Yanzu haka jiragen ƙasashen waje na barazanar dakatar da zirga-zirga zuwa Najeriya saboda lalacewar filin jirgi da hanyoyin sauka da tashi,”
In ji shi
2027: Keyamo ya ce Tinubu zai yi nasara
A wani rahoton, kun ji cewa ministan sufurin jiragen saman Najeriya ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a 2027.
Festus Keyamo ya ce Bola Tinubu yana da manyan 'yan siyasa da suka hada da gwamnoni da suka tsaya masa a Arewa.
Ministan ya kara da cewa haduwar Peter Obi da Atiku Abubakar a karkashin jam'iyyar ADC ba zai hana APC cin zabe a 2027 ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

