Babu Dadi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon da Mata yayin Wani Hari a Zamfara

Babu Dadi: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon da Mata yayin Wani Hari a Zamfara

  • 'Yan bindiga sun tafka ta'asa bayan sun kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara
  • Miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mata da suka fita neman itace . a cikin daji a kauyen Moriki
  • Jami'an tsaro da suka hada da dakarun sojoji da 'yan sa-kai sun fara yunkurin ganin sun kubutar da matan daga hannun 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da mata 23 a wani hari da suka kai a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun sace matan ne a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara yayin da suke cikin daji suna tattara itacen girki.

'Yan bindiga sun sace mata a Zamfara
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi, 3 va watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina, an dakile hare hare 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka sace mata a Zamfara

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da faruwar wannan lamarin a ranar Lahadi, inda suka bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Juma’a, 2 ga watan Agusta, da misalin karfe 1:30 na rana.

A cewar majiyoyin, matan da aka sace duka mazauna garin Moriki ne, kuma ‘yan bindigan sun yi musu kwanton-bauna ne a cikin dajin da ke wajen gari inda suka tare su yayin da suke aikin samo itace.

Yan bindigan sun tafi da wadannan mata zuwa wani wurin da ba a sani ba, kuma har yanzu ba a iya gano inda suke ba.

Dakarun sojoji sun kai dauki

Bayan samun rahoton faruwar lamarin, dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma tare da hadin guiwar jami’an tsaro na yankin da kuma ‘yan banga sun kaddamar da wani gagarumin samame domin kubutar da matan daga hannun masu garkuwa da su.

Majiyar tsaro ta kara da cewa duk matakan da suka kamata an fara dauka domin ganin cewa an ceto rayukan wadannan mata ba tare da wani rauni ba, sannan kuma a kamo wadanda suka aikata wannan aika-aikar domin su fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Jagororin 'yan bindiga sun gwavza fada a Zamfara, an samu asarar rayuka

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mata a Zamfara
'Yan bindiga sun sace mata a Zamfara Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lamarin ya kara tayar da hankalin al’ummar yankin, musamman ma dangi da ‘yan uwa na wadanda aka sace, wadanda ke cikin damuwa da fatan gwamnati da hukumomin tsaro za su dauki matakin gaggawa.

Wannan lamari na kara nuna irin yadda tsaro ke kara tabarbarewa a wasu sassan Zamfara, musamman ma a yankunan karkara inda mata da yara ke cikin hadari a duk lokacin da suka fita neman abinci ko itacen girki.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarum sojoji sun samu nasarar yin raga-raga da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne bayan sun yi wani artabu mai zafi da su a cikin kasurgumin daji.

Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar kwato makamai da babura daga hannun 'yan ta'addan masu tayar da kayar baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng