An Naɗa Ɗan Gwamna, Ministan Buhari da Wasu Mutum 4 a Matsayin Sababbin Hakimai a Katsina

An Naɗa Ɗan Gwamna, Ministan Buhari da Wasu Mutum 4 a Matsayin Sababbin Hakimai a Katsina

  • Masarautar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ta sanar da naɗin sababbin hakimai shida a faɗin jihar
  • A sanarwar da sakataren masarautar ya fitar ranar Asabar, ɗan Gwamna Diko Raɗɗa na cikin waɗanda aka naɗa a matsayin hakimai
  • Haka zalika, tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya zama sabon Marusan Katsina, hakimin Shargalle a ƙaramar hukumar Dutsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya naɗa sababbin hakimai shida da aka ƙirƙira a kwanakin baya a jihar.

Ɗan mai girma gwamnan Katsina, Muhammad Dikko Umaru Raɗɗa na cikin waɗanda aka naɗa a matsayin sababbin hakimai a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Masarautar Katsina ta nada sababin hakimai 6 Hoto: Malam Abdul Maje
Source: Facebook

Masarautar Katsina ta naɗa sababbin hakimai

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa masarautar Katsina ta kuma naɗa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika a matsayin hakimi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya zama na farko da zai shiga jam'iyyar haɗaka, ADC? An samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana waɗanda aka naɗa sababbin hakiman ne a wata sanarwa da sakataren masarautar Karsina, Alhaji Bello Ifo ya fitar ranar Asabar, 2 ga watan Agusta, 2025.

Yadda aka ƙirkiro ƙarin hakimai 6 a Katsina

Hakan dai na zuwa ne bayan gwamnatin Katsina karƙashin jagorancin Malam Dikko Raɗɗa ta kirkiro sababbin hakimai a wasu yankuna a ƴan watannin da suka gabata.

Tuni dai Gwamna Dikko Raɗɗa ya tura kudirin ƙirkiro waɗannan sababbin hakimai ga Majalisar Dokokin Jihar Katsina, kuma ta amince da kudirin.

Wannan mataki dai ya yu wa al'ummar jihar Katsina daɗi musamnan waɗanda suke yankunan da aka samar da hakimai, inda mutane suka rika yabon mai girma gwamna.

Ɗan Gwamna da Hadi Sirika sun zama hakimai

A cewar sanarwar, masarautar Katsina ta amince da naɗin Sanata Hadi Sirika a matsayin sabon Marusan Katsina, Hakimin Shargalle a ƙaramar hukumar Dutsi.

Hadi Sirika dai ya yi aiki a matsayin minista kula da harkokin sufurin jiragen sama a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Yaƙi da ƴan ta'adda: Gwamnatin tarayya za ta ɗauki matasa 13000 aikin sojan ƙasa

Muhammad Radda, ɗan Gwamna Dikko Radda, shi ne sabon Gwagwaren Katsina, Hakimin Radda a ƙaramar hukumar Charanchi, rahoton Vanguard.

Sauran sababbin Hakiman da aka nada sun haɗa da:

  • Alhaji Sanusi Kabir-Usman, Karshin Katsina, Hakimin Shinkafi a ƙaramar hukumar Kaita.
  • Alhaji Ahmad Abdulmumini-Kabir, Dan-Majen Katsina, Hakimin Dankama, a ƙaramar hukumar Kaita.
  • Alhaji Abubakar Dardisu, Sarkin Mudurun Katsina, Hakimin Muduru, a ƙaramar hukumar Mani.
  • Alhaji Gambo Abdullahi Dabai, Dausayin Katsina, Hakimin Dabai, a ƙaramar hukumar Danja.

Masarautar Katsina ta kuma ƙara da cewa nadin sababbin hakiman ya fara aiki ne daga ranar Asabar.

Sarkin Katsina da Malam Dikko Radda.
Sarkin Katsina ya ɓada ɗan Gwamna Radda a matsayin hakimi Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Wani ɗan garin Dabai, ɗaya daga cikin wuraren da aka ba hakimi, Abdul Tukur ya shaidawa Legit Hausa cewa sun yi farin ciki da wannan naɗi.

Ya ce wanda aka naɗa a matsayin hakimin Dabai na farko, Alhaji Gambo Abdullahi mutumin kirki ne, ya kuma godewa gwamna da masarautar Katsina.

"Wannan ci gaba ne da muka daɗe muna jira, saura ma a bamu ƙaramar hukuma. Mai girma gwamna ya tabbatar mana da alƙawarinsa, muna masa fatan alheri," in ji shi.

Kara karanta wannan

Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

An naɗa sabon Sarkin Katsinan Gusau

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya nada Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau (Sarkin Gusau) da ke jihar Zamfara.

Sabon Sarkin zai maye gurbin mahaifinsa, marigayi Dr. Ibrahim Bello wanda Allah ya yiwa rasuwa a safiyar ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 yana da shekara 71.

Gwamna Lawal ya amince da naɗin ne bisa shawarar masu zaben Sarki na masarautar Gusau, tare da bin dokoki da al’adun gargajiya na Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262