Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Waiwayi Manyan Asibitocin Jihar
- Gwamnatin jihar Katsina ta dauki damarar samar da tsaro a manyan asibitoci domin kare rayukan ma'aikata da masu jinya
- A yayin taron majalisar zartarwa, gwamnatin ta amince da kashe N703m don gina katangu a wasu manyan asibitoci na kananan hukumomin da ke da barazanar tsaro
- Wannan yunkurin dai na zuwa ne yayin da wasu kananan hukumomin jihar ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-hare daga 'yan bindiga
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta amince da kashe Naira miliyan 703 domin sake gina katangu da kuma sanya shingen tsaro a manyan asibitoci.
Gwamnatin ta amince a yi aikin ne a manyan asibitoci guda 14 da ke wasu kananan hukumomin jihar masu fama da rashin tsaro.

Source: Facebook
Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri, Dakta Sani Magaji-Ingawa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a garin Katsina, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron majalisar zartarwa ta jihar.
A ina za a gina katangun?
Sani Magaji-Ingawa ya bayyana cewa, kananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Kankara, Malumfashi, Faskari, Jibia da Funtua.
Sauran su ne Kafur, Dandume, Musawa, Batsari, Dutsin-ma, Kurfi, Danmusa, birnin Katsina, da kuma babban asibitin Amadi Rimi.
"Wannan aikin inganta gine-ginen wani ɓangare ne na shirin da gwamnatinmu ke aiwatarwa domin ƙarfafa cibiyoyin lafiya a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, da kuma tabbatar da tsaron ma’aikata da marasa lafiya."
- Sani Magaji-Ingawa
Kwamishinan ya ƙara da cewa, majalisar zartarwa ta amince da ɗaukaka cibiyar lafiya ta Mai’adua zuwa cikakken babban asibiti, a kan kuɗin da ya kai Naira biliyan 1.3.
Haka zalika, Sani Magaji-Ingawa ya bayyana cewa majalisar ta kuma amince da kashe Naira biliyan 18.5 domin gina muhimmin titin Rafin Iya–Tashar Bawa–Sabuwa, rahoton TVC News ya tabbatar.

Kara karanta wannan
Gwara Haka: Jagororin 'yan bindiga sun gwavza fada a Zamfara, an samu asarar rayuka
Ya ce da zarar an kammala aikin, titin zai inganta ayyukan tsaro, sauƙaƙa jigilar kayan noma, da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci da tattalin arziki a yankunan da ya ratsa.
"Muna ɗaukar matakai domin haɗa al’ummomi, tallafawa manoma, da faɗaɗa hanyoyin cikin gida na jiharmu domin samun ci gaba mai ɗorewa".
- Sani Magaji-Ingawa

Source: Facebook
Aikin zai taimaka
Ibrahim Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa sake gina katangu a asibitocin zai taimaka sosai wajen samar da tsaro.
"Eh gaskiya ina ganin idan aka yi aikin zai taimaka sosai kan wajen samar da tsaro. Dama bai kamata a ce an bar asibitoci babu katangu ba."
"Muna fatan Allah ya kawo mana karshen wadannan matsalolin."
- Ibrahim Kabir
Karanta wasu labaran kan rashin tsaro a Katsina
- 'Su ƙona gidajenmu, su harbe mu:' Yadda ƴan bindiga su ka dawo Katsina da ƙarfinsu
- Rashin tsaro: Jami'an sojoji, ƴan sanda da dakarun CWC sama da 130 sun 'mutu' a Katsina
- An gwabza fada tsakanin 'yan sanda da 'yan ta'adda a Katsina, an rasa rayuka
An sallami gwamnan Katsina daga asibiti
A wani labarin kuma, kun ji cewa likitoci sun sallami gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda daga asibiti bayan ya yi jinya.
An dai kwantar da gwamnan ne a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja sakamakon hatsarin motar da ya ritsa da shi.
Likitocin da suka duba gwamnan sun ba da tabbacin cewa ya samu cikakkiyar lafiya kuma zai iya komawa bakin aiki.
Asali: Legit.ng

