Wata Sabuwa: Jihar Neja Ta Maka Gwamnatin Tinubu Kara gaban Kotun Koli
- Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Umar Bago ta shigar da gwamnatin tarayya kara a gaban Kotun Koli
- Ta shigar da karar ne kan kin sanya ta cikin jerin jihohin da ke samun kaso 13% na daga abin da aka samu daga albarkatun da suke samarwa
- Gwamnatin ta bukaci kotun da ta sanya a sanya ta cikin jerin, duba da irin dumbim albarkatun da take samarwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja ta kai ƙarar Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Koli.
Gwamnatin Neja ta kai karar ne don kalubalantar kin sanya ta daga cikin jihohin da ke cin gajiyar kaso 13% cikin 100% na haƙƙin samar da albarkatun kasa.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce jihar ta shigar da ƙarar ne ta hannun tawagar lauyoyinta ƙarƙashin jagorancin Mohammed Ndarani (SAN).
An sanya babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a a matsayin wanda ake ƙara shi kaɗai a shari’ar, rahoton The Guardian ya tabbatar.
An yi karar gwamnatin Tinubu a kotu
Masu shigar da ƙarar sun roƙi Kotun Koli da ta tantance ko jihar Neja ba ta cancanci a saka ta cikin jerin jihohin da ke samar da albarkatun ƙasa ba, don haka ba ta da haƙƙin samun kason bisa tanadin sashe na 162(2) na kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa gyara.
Haka kuma, sun nemi kotun ta fassara kuma ta aiwatar da tanadin sashe na 232 (1) da (2) na kundin tsarin mulki, domin tilasta wa gwamnatin tarayya ta haɗa ta a cikin masu samun kason, bisa dokar rabon kudade ta shekarar 2004.
Jihar ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen haɗa kuɗaɗen da ake samu daga albarkatun da ake samarwa daga madatsun ruwan wutar lantarki da ke cikin yankinta.
Ta bayyana cewa sun taka rawa wajen samar da wutar lantarki ga layin rarraba wuta na kasa tun daga shekarar 1968.
Jihar ta ce dalilin da ya sa ta ɗauki babban lauyan gwamnatin tarayya a matsayin wanda take ƙara shi kaɗai, shi ne saboda shi ne ke da hurumin ba da shawarwari na shari’a da kuma wakiltar gwamnatin tarayya, ciki har da Akanta Janar na tarayya.
Ta kuma zargi wanda ake ƙarar da gazawa wajen ba shugaban ƙasa sahihiyar shawara, musamman ta fuskar tabbatar da adalci wajen rabon albarkatu bisa ga yanayin da ake ciki a yanzu.

Source: Facebook
Me gwamnatin Neja ke so a yi mata?
Gwamnatin ta ce ya kamata a sanya ta cikin jerin jihohin duba da yawan kuɗin shiga da jihar Neja ke samarwa ta hanyar wadannan madatsun ruwan da take da su.
Saboda haka, masu shigar ƙarar sun roƙi Kotun Koli da ta tsoma baki ta kuma bayar da umarnin haɗa jihar Neja cikin jerin jihohin da ke cin gajiyar kaso 13% na albarkatun ƙasa.
A halin yanzu dai, ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba kamar yadda rahotanni suka nuna.
An ba 'yan Arewa shawarar zaben Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Arewa Think Thank (ATT), ta bukaci 'yan Arewa su goyi bayan tazarcen mai girma Bola Tinubu a 2027.
Ta bayyana cewa yankin Arewa bai da wani dalilin da zai sanya ya ki goyon bayan sake zaben shugaban kasan ba.
Kungiyar ta nuna cewa Shugaba Tinubu ya aiwatar da ayyukan ci gaba a yankin Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng


