'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki kan Manoma a Sokoto, an Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan manoman da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Sokoto
- Miyagun 'yan bindigan wadanda ake zargin na kungiyar Lakurawa ne sun kai harin ne a wani kauye da ake kira Ayama
- Dakarun sojoji sun kai agajin gaggawa bayan samun labarin harin da 'yan bindigan suka kai, inda aka yi musayar wuta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - ’Yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Lakurawa ne sun kai mummunan hari a ƙauyen Ayama da ke cikin gundumar Balle a jihar Sokoto.
A yayin harin da 'yan bindigan suka kai, sun kashe manoma biyu a ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Yadda 'yan bindiga suka kashe manoma
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da waɗanda abin ya shafa ke aiki a gonarsu da ke bayan ƙauyen.
Manoman dai suna ci gaba da aikin gona na yau da kullum ba tare da sanin barazanar da ke tafe ba lokacin da lamarin ya auku.
Maharan sun iso ne a kan babura, dauke da muggan makamai irin su bindigogi na zamani, inda suka bude wuta ba tare da wani jinkiri ba a kan manoman.
A sakamakon haka, aka kashe Tukur Muhammed, mai shekara 30, da Sa’ad Muhammed, mai shekara 25, nan take a wurin.
Dakarun sojoji sun kai dauki
Bayan samun rahoton harin, dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yanma sun hanzarta isa wajen da abin ya faru, inda suka shiga fafatawa da ’yan bindigan.
Duk da ƙoƙarin sojojin, maharan sun samu nasarar tserewa ta kan iyaka zuwa Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.
An garzaya da gawarwakin mutanen biyu da aka kashe zuwa asibiti domin yin rajista da kuma shirye-shiryen jana’izar su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Source: Original
A halin yanzu, hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara sintiri da kai dauki cikin gaggawa a yankin domin dakile duk wani yunkurin kai harin ramuwar gayya ko wani sabon hari daga ’yan bindiga.
Hukumomi da jami’an tsaro sun kuma bukaci mazauna yankin da su kasance masu lura da kewaye tare da bayar da rahoto cikin gaggawa idan suka ga wani abu da ba su yarda da shi ba.
Wannan hari na ƙara nuna bukatar tsaurara matakan tsaro da kuma haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro don samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
'Yan bindiga sun hallaka sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaro ciki har da sojoji a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun hallaka jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sa-kai bayan sun yi musu kwanton bauna.
Lamarin dai ya auku ne bayan da jami'an suka je kai daukin gaggawa bayan samun rahoton shirin 'yan bindiga na kai hari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

