"Ya Cika Su": Minista Ya Yi Bayani kan Alkawuran da Tinubu Ya Yi Wa Arewa
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya tabo batun alkawuran da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yankin Arewa
- Mohammed Idris ya bayyana cewa yankin Arewa bai bin Shugaba Tinubu bashi kan alkawuran da ya dauka kafin zaben 2023
- Ya nuna cewa shugaban kasan ya saka 'yan Arewa masu yawa a cikin gwamnatinsa domin yin aiki tare da shi, akasin zargin wasu mutane
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Alhaji Mohammed Idris, ya yi magana kan alkawuran da Shugaba Bola Tinubu ya daukarwa yankin Arewa.
Mohammed Idris ya ce Shugaba Tinubu ya cika yawancin alkawurran da ya daukarwa yankin Arewa, kuma zai ci gaba da yin wasu ayyukan.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a shirin “Hannu da Yawa” na gidan Rediyo Najeriya Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka' - Minista
Ministan ya bayyana cewa Tinubu ya yi wa Arewa alkawura kafin zaben 2023, kuma ya cika su, rahoton Vanguard ya tabbatar.
"Kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Tinubu ya je gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello, inda ya yi alkawurra da dama ga yankin Arewa kan harkokin tsaro, ilimi da kuma noma."
"Ya kamata a sani cewa bayan da ya lashe zaben, Shugaba Tinubu ya cika alkawurransa ga yankin Arewa; ya nada mutane da dama daga Arewa cikin gwamnatinsa."
"Cikin su akwai ministan tsaro, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, babban hafsan tsaro, ministocin moma, harkokin mata, lafiya, al’adu da tattalin arzikin fikira, ni kaina da wasu da dama. Hakika, mun haura mutum 60 daga Arewa da ke aiki tare da Tinubu."
"Yanzu shekaru biyu kenan da shugabancinsa, kuma mun zo wannan cibiyar tare da ministoci fiye da 20 da wasu, domin bayyana irin alkawurran da aka cika da kuma wasu muhimman nasarori da suka shafi ba Arewa kadai ba, har da ƙasar baki ɗaya."
- Mohammed Idris

Source: UGC
Minista ya ce Tinubu bai yi watsi da Arewa ba
Mohammed Idris ya ce akwai jita-jita da bayanan da ba su dace ba da ke cewa Shugaba Tinubu ya yi watsi da yankin Arewa.
"Amma yau mun bayyana kuma an gani da ido cewa wannan zance ba gaskiya ba ne. A gaskiya, ya yi abin a yaba wa Arewa."
- Mohammed Idris
Ministan ya jaddada cewa tawagar za ta ci gaba da wayar da kan jama'a, musamman mazauna Arewa, kan muhimman nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu.
Tukur Lawal ya shaidawa Legit Hausa cewa jami'an gwamnati suna fadin kawai abin da ya yi musu dadi ne kawai a rai.
"Ta ya za a ce Tinubu ya cika alkawuran da ha daukarwa Arewa? Me talakan Arewa ya amfana da shi a mulkin?"
"Ya kamata mutanen su rika jin tsoron Allah su daina fadin abin da ba daidai ba ne."
- Tukur Lawal
Uba Sani ya magantu kan tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ari bakin gwamnoni kan tazarcen mai girma Bola Tinubu a 2027.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa babu wani gwamna da zai fito ya kalubalanci sake zaben Tinubu a zaben shugaban kasa da ake tunkara.
Uba Sani ya nuna cewa ba a taba samun shugaban kasa ba kamar Tinubu wanda ya goyi bayan gwamnoni da gwamnatocin jihohin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


