Hankula Sun Tashi bayan Barkewar Rikicin Kabilanci Abuja, an Tafka Barna

Hankula Sun Tashi bayan Barkewar Rikicin Kabilanci Abuja, an Tafka Barna

  • An samu barkewar rikicin kabilanci a garin Abuja wanda ya jawo asarar rai da kona gidaje masu yawa
  • Lamarin ya auku ne tsakanin Fulani da 'yan kabilar Gwari a kauyen Gurfata da ke karamar hukumar Gwagwalada ta Abuja
  • Fadan wanda ya fara tsakanin mutane biyu, ya rikide zuwa babban lamari da ya jawo aka kona gidaje akalla guda 31

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadan kabilanci ya barke tsakanin Fulani da kabilar Gwari a ƙauyen Gurfata da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada, a Abuja.

Barkewar fadan ya jawo sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da kona gidaje fiye da 31.

Mutane sun rasu sakamakon rikicin kabilanci a Abuja
An samu barkewar rikicin kabilanci a Abuja Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin kabilanci ya jawo asarar rai a Abuja

Kara karanta wannan

Ruwa da iska mai ƙarfi sun kifar da jirgi bayan ya ɗauko fasinjoji a jihar Jigawa

Rahotanni sun ce rikicin wanda ya faru a ranar Talata, ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin wani Bafillace mai suna Shaibu Adamu da wani manomi dan kabilar Gwari mai suna Sa’adu, kan hanyar da ta ratsa gonar Sa’adu.

Majiyoyi daga cikin kauyen sun ce rigimar ta fara ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe, lokacin da Adamu ya yi yunkurin ketara gonar Sa’adu ba tare da shanu ba.

Sai dai Sa’adu ya hana shi, inda ya buƙaci ya bi wata hanya ta daban. Hakan ya sa suka fara cacar baki, wadda daga bisani ta rikide zuwa faɗa, inda su duka biyun suka samu raunuka 'yan kaɗan.

Wannan lamari ya sake tayar da ƙiyayyar kabilanci a ƙauyen, inda dukkan bangarorin biyu suka fara taruwa don nuna goyon baya ga mutanensu.

Lamarin ya kara muni ne lokacin da Adamu Ibrahim, ɗan uwan Shaibu, ya kai wa wani dan kabilar Gwari mai suna Dahiru Yakubu farmaki da adda.

An garzaya da Dahiru Yakubu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja, inda daga baya ya rasu sakamakon raunin da ya samu.

Mutuwar Dahiru Yakubu ta tayar da hankula, inda wasu matasa daga bangaren Gwari suka kai farmaki kan sansanin Fulani da ke Gurfata, suka ƙone gidaje 31, sannan suka jikkata mutane akalla uku.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Saurayi ya sari tsohuwar budurwarsa da adda, ya kashe mahaifiyarta

Fulani da 'yan kabilar Gwari sun yi rikici a Abuja
Rikicin kabilanci ya jawo asarar rai a Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojojin Najeriya sun kai dauki

Daga bisani, dakarun sojojin Najeriya tare da wasu jami’an tsaron haɗin gwiwa sun isa yankin domin dakile tashin hankali da dawo da zaman lafiya.

Hukumomi sun roƙi al’ummomin biyu da su kwantar da hankalinsu tare da gujewa ɗaukar fansa.

A halin yanzu, ana ci gaba da ƙoƙarin sasanta bangarorin da nufin hana sake ɓarkewar rikici.

Rikicin kabilanci ya jawo asarar rayuka a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani rikicin kabilanco da ya barke a jihar Taraba ya asarar rayukan mutane da dama.

Rikicin wanda ya barke a karamar hukumar Karim-Lamido, ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane akalla 40, yayin da wasu da dama suka rasa matsuguninsu.

Lamarin da ya auku ne a tsakanin Fulani makiyaya da manoma 'yan kabilar Bandawa kan barnar da shanu suka yi a gona.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng