Amurka Ta Gargadi Gwamnonin Najeriya kan Rashin Kula da Talakawa

Amurka Ta Gargadi Gwamnonin Najeriya kan Rashin Kula da Talakawa

  • Ofishin jakadancin Amurka ya yi suka kan yadda wasu gwamnoni ke kashe makudan kudi a gidajen gwamnati duk da halin kunci da ake ciki
  • Rahoto ya bayyana cewa yayin da Bola Tinubu ke bukatar mutane su yi hakuri, manyan masu mulki ba sa nuna hakan a aikace
  • Misalan da aka bayar sun hada da Seyi Makinde da Inuwa Yahaya da suka ware daruruwan biliyoyi kan gine-gine a gidajen gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya soki yadda wasu gwamnoni ke ci gaba da kashe makudan kudi a gidajen gwamnati duk da matsin tattalin arziki da talakawa ke ciki.

Wannan yana kunshe ne a cikin wani rahoto mai dauke da bayanai kan yadda shugabannin Najeriya ke kashe kudi a ayyuka marasa muhimmanci.

Kara karanta wannan

Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu

Shugaban Amurka, Donald J Trump
Shugaban Amurka, Donald J Trump. Hoto: White House
Source: Getty Images

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da sanarwa kan lamarin ne a wani sako da ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rahoton, an bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu yana kiran 'yan Najeriya da su yi hakuri saboda sauye-sauyen tattalin arziki da ya kawo.

Amma a gefe guda, gwamnoni da sauran manyan jami'an gwamnati ba su bin wannan hanyar da ya zaba.

Gwamna Makinde na kashe biliyoyi a gini

Daya daga cikin misalan da rahoton ya bayar shi ne na gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda ya amince da kashe Naira biliyan 63.4 domin gyaran gidan gwamnati.

Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman ganin cewa yawancin ma’aikatan jihar da sauran mazauna Oyo na fama da tsadar rayuwa da karancin albashi.

Jama’a da dama na ganin bai kamata a kashe irin wannan kudi a lokacin da mutane ke cikin kunci ba.

Gwamna Inuwa da sababbin gine gine

Kara karanta wannan

Ana zaman ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin 'yan Arewa da jami'an gwamnatin Tinubu a Kaduna

A Gombe kuwa, rahoton ya bayyana cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya ware Naira biliyan 14.9 domin sabunta gidan gwamnati.

Baya ga haka, Inuwa Yahaya ya ware Naira biliyan 14.23 domin gina sabon ginin majalisar dokokin jihar.

Daily Trust ta wallafa cewa masu sharhi sun nuna damuwa da cewa irin wannan kashe kudin ba ya nuna kulawa ga halin da jama’a ke ciki.

Mashigar gidan gwamnatin Gombe da aka sabunta
Mashigar gidan gwamnatin Gombe da aka sabunta. Hoto: Usman Usman
Source: Facebook

Korafin Amurka kan gwamnonin Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka ya bayyana cewa rashin gaskiya da kin koyi da yanayin da ake ciki yana gurbata amana tsakanin gwamnati da jama’a.

Haka zalika, kungiyoyin da ke fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci sun nuna damuwa matuka kan lamarin.

Martanin Farfesa Ochonu daga Amurka

Wani Farfesa dan Najeriya da ke zaune a Amurka, Moses Ochonu, ya bayyana cewa wannan martani daga Amurka na iya saka gwamnoni su fara jin tsoron Allah.

Ya wallafa a Facebook cewa:

“Tun da har ofishin jakadancin Amurka ya shiga wannan batu da muke ta kururuwa a kai, to watakila a yanzu za a dauki korafin mutane da muhimmanci.”

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya hararo babban rikici a Najeriya idan aka yi magudi a zaben 2027

Kasar Iran ta yi wa Amurka martani

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta yi taron tunawa da sojojinta da sauran 'yan kasa da suka rasu a yakin da ta yi da Isra'ila.

Iran ta ce sadaukarwar da sojojin suka yi bai tafi a banza ba kuma ya kara fito da darajar kasar a idon duniya.

Kasar ta bayyana cewa Amurka da kawayenta suna yaki da ita ne domin cigaba da suke samu ba wai don mallakar makamin nukiliya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng