Ba Dadi: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka

Ba Dadi: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka

  • An samu asarar rayuka bayan da 'yan bindiga suka yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a jihar Plateau
  • Farmakin da 'yan bindigan suka kai kan jami'an tsaron ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji da 'yan sa-kai a karamar hukumar Wase
  • Lamarin da ya auku bayan da jami'an tsaron suka je kai daukin gaggawa bayan sun samu rahoton shirin 'yan bindiga na kai hari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu da 'yan sa-kai biyu a wani hari a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe jami'an tsaron ne a ranar Talata da rana a kusa da Dogon Ruwa, wani kauye da ke cikin gundumar Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kashe sojoji a Plateau
Ba Dadi: 'Yan bindiga sun hallaka sojoji a Plateau Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Wasu mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa 'yan bindigan sun kwashe bindigogi mallakar sojojin da suka kashe.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ritsa 'yan ta'addan Boko Haram a daji, an kashe miyagu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kashe sojoji a Plateau

Sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana, a lokacin da sojoji da 'yan sa-kai ke bin sahun ‘yan bindigan da suka yi ƙoƙarin kai hari a yankin.

Sarkin Safiyo, Abdullahi Yakubu, wanda Dogon Ruwa ke ƙarƙashinsa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A yayin da yake Allah wadai da harin, ya ce sojoji da 'yan sa-kam sun fada tarkon ‘yan bindigan ne ba zato ba sammani.

"An samu rahoton cewa ‘yan bindiga na shirin kai hari Dogon Ruwa. Mutane suka gaggauta sanar da jami’an tsaro, wadanda suka tashi da gaggawa zuwa inda aka ce an gan su."
"Amma ba tare da sanin su ba, ‘yan bindigan sun yi kwantan-ɓauna, suka bude musu wuta wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu da 'yan sa-kai biyu."

- Abdullahi Yakubu

'Yan bindia sun farmaki sojoji a Plateau
'Yan bindiga sun kashe sojoji a Plateau Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana tsoron an kwashe kayan sojoji

Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Sale, ya bayyana cewa bayan kashe jami’an tsaron, ‘yan bindigan sun kwashe bindigoginsu da kayan sojoji.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da ƴan bindiga, an cafke wani baƙon ɗan ta'adda a Yobe

Ibrahim Sale ya ƙara da cewa, faruwar wannan al’amari ya haddasa fargaba da damuwa a tsakanin mazauna Dogon Ruwa da sauran kauyukan da ke makwabtaka da su.

A halin da ake ciki, mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai mayar da martani kan saƙon da aka tura masa kan harin ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a Borno.

Sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne bayan sun yi musu kwanton bauna a karamar hukumar Bama.

Hakazalika, jami'an tsaron sun kwato kayayyaki masu yawa da tare da raunata wasu daga cikin 'yan ta'addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng