An Cakawa Jami'ar NSCDC Wuƙa a Abuja, Asibitoci Sun Ƙi Karɓarta har Ta Mutu

An Cakawa Jami'ar NSCDC Wuƙa a Abuja, Asibitoci Sun Ƙi Karɓarta har Ta Mutu

  • Wasu bata-gari sun cakawa wata jami’ar NSCDC, Akpan Blessing wuka a gaban gidanta da ke Abuja, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta
  • An ce an kai ta asibitoci daban daban amma ba a karɓe ta ba saboda babu rahoton ‘yan sanda, abin da ya sa ta zubar da jini har ta mutu
  • Rahoto ya nuna cewa wasu asibitocin sun ki karɓarta duk da an nuna masu katin aikinta, yayin da rundunar ta yi shiru kan lamarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata jami’ar hukumar tsaron farar hula ta Najeriya (NSCDC) mai suna Akpan Blessing, ta mutu bayan an caka mata wuka a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu bata-gari ne suka caka wa Blessing wuka a gaban gidanta da ke Piawe, Bwari, Abuja, da safiyar ranar Talatar makon jiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare hanya, an yi awon gaba da daliban kwaleji

Wasu bata gari sun kashe jami'ar hukumar NSCDC a Abuja
Jami'an hukumar NSCDC sun jera layi a wani bikinsu da aka gudanar. Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

An ki karbar jami'ar NSCDC a asibitoci

Ma'aikatan asibitin gwamnati na Bwari da ke bakin aiki a lokacin da aka kai jami'ar ne suka tabbatar da mutuwarta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin abokanta da suka yi magana a ranar Litinin sun ce an garzaya da mamaciyar zuwa asibitoci daban-daban, amma suka ki karɓar ta saboda babu rahoton ‘yan sanda.

Wata abokiyar marigayiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce asibiti na farko da aka kai Blessing shi ne asibitin Gabriel, kafin daga bisani a kai ta asibitin St. Theresa, wadanda suke a Bwari.

Cikin ɓacin rai, ta ce jami’ar NSCDC din ta zubar da jini mai yawa kafin a karɓe ta a asibitin gwamnati na Bwari, inda a nan ne aka tabbatar da mutuwarta.

Kawar jami'ar da aka kashe ta yi magana

Abokiyar jami'ar NSCDC din ta ce:

Kara karanta wannan

Jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife a tsakiyar kogi, rayuka sun salwanta

“Abin takaici ne yadda muka rasa Ofisa Blessing, kamar yadda muke kiranta, domin asibitoci sun ki karbarta saboda kawai babu rahoton 'yan sanda.
“Suna ganin mutum na gargarar mutuwa, amma sun nace sai an kawo rahoton ‘yan sanda kafin a fara ba ta agajin gaggawa.
“Gaskiya wannan abin bakin ciki ne. Baya ga haka, jami’ar tsaro ce. Mun nuna musu katin shaidarta na aiki, amma duk da haka sun ki karɓar ta. Hakan ya sa muka yi ta yawo da ita asibitoci daban-daban har ta rasu.”

Da aka tambaye ta yadda lamarin ya faru, wata abokiyar Blessing ta ce:

“Tana kan hanya ne wasu suka nemi su kwace mata kayanta amma ta ki sakar masu, shi ne suka caka mata wuka domin su kwace kayan.”
Hukumar NSCDC ba ta yi magana game da jami'arsu da aka kashe a Abuja ba
Dr. Ahmed Abubakar Audi, shugaban hukumar tsaron fararen hula (NSCDC). Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

Yadda aka cakawa jami'ar NSCDC wuka

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya a babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta ce a tuntuɓi hukumar NSCDC domin jin matsayinsu kan lamarin.

Adeh, wadda sufuritandan ‘yan sanda ce, ta bayyana cewa hukumar NSCDC na iya gudanar da bincikenta kai tsaye, domin babu rahoton da aka kai ofishinsu game da lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke budurwar da ta kashe yara 2, an ceto jariri

Haka zalika, kakakin NSCDC na kasa, Babawale Afolabi, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar reshen Abuja ce za ta bayar da cikakken bayani kan lamarin.

Sai dai kwamandan NSCDC na Abuja, Olusola Odumosu, bai amsa kiran da aka yi masa ba, kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai mayar da martani ga sakon da aka aika masa ba.

'Yan daba sun farmaki ofishin NSCDC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ƴan daba sun kai hari a ofishin hukumar NSCDC da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

An rahoto cewa an kai harin ne bayan zargin wani mai satar waya ya rasa ransa a hannun wanda ya yi ƙoƙarin sace masa salula.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NSCDC ya bayyana harin da aka kai ofishin a matsayin abin bakin ciki, yana mai cewa ana gudanar da bincike a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com