'Yan Ta'adda Sun Kai Farmaki a Neja, an Yi Awon Gaba da Bayin Allah

'Yan Ta'adda Sun Kai Farmaki a Neja, an Yi Awon Gaba da Bayin Allah

  • 'Yan ta'adda dauke da makamao sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Kontagora ta jihar Neja
  • Tsagerun sun yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a kauyen Usubu
  • Daga cikin mutanen da aka sace har da wata mata tare da jaririnta wanda yake da da watanni shida a duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu miyagu dauke da makamai da ake zargin 'yan ta’adda ne sun sace mutane shida a jihar Neja.

'Yan ta'addan sun sace mutanen ne ciki har da wata uwa da jaririnta mai watanni shida, a wani samame da suka kai da tsakar dare a yankin Usubu da ke karamar hukumar Kontagora a jihar Neja.

'Yan ta'adda sun sace mutane a Neja
'Yan ta'adda sun yi garkuwa da mutane a Neja Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga sun shiga cikin gona, sun ɗauke malami da wasu mutum 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace mutane a Neja

Rahoton ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:20 na daren ranar Asabar, 26 ga watan Yulin 2025.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa waɗanda aka sace sun haɗa da, Nasiru Muhammed, mai shekaru 30, Abdulrahman Adamu, mai shekaru 25, Abdul Baqi Muhammed, mai shekaru 20.

Sauran sun hada da Ubaida Yahaya, mai shekaru 35, tare da ɗanta ƙarami, Nazifi Yahaya, mai wata shida da Umaima Nura, mai shekaru 25.

'Yan ta'addan dai sun shigo yankin ne a boye da makamai a hannunsu, inda suka tursasa wa mutanen da suka sace su bi su zuwa cikin daji.

Maharan sun shiga kauyen cikin sauri, suna harbe-harbe a sama domin tayar da hankalin mutane, kafin su shiga wasu gidaje su sace mutanen.

Jami'an tsaro sun ziyarci inda lamarin ya auku

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kai ziyara yankin da gaggawa, kuma an fara farautar waɗanda suka aikata wannan danyen aiki.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: 'Yan sanda sun kama sojoji a wajen da ba a tsammani

Rundunar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki tare domin gano inda masu laifin suke da kuma kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a wasu sassan jihar Neja, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Al’ummar yankin sun bayyana damuwarsu kan yadda hare-haren da ake kai musu ke kara ƙaruwa, suna kuma kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

An kuma roƙi a ɗauki matakai sosai kan wannan lamarin domin gujewa ci gaba da samun asarar rayuka da kuma rashin zaman lafiya a yankin.

'Yan bindiga sun farmaki manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun kai harin ne a wasu kauyuka uku da ke karamar hukumar Bakura ta jihar.

A harin da suka kai daya daga cikin kauyukan, sun hallaka manoma hudu bayan sun bude musu wuta a cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng