Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji Ya Kife a Tsakiyar Kogi, an Samu Asarar Rayuka

Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji Ya Kife a Tsakiyar Kogi, an Samu Asarar Rayuka

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja
  • Hatsarin jirgin ruwan ya auku ne bayan da ya kife a tsakiyar kogi a ranar Asabar, 25 ga watan Yulin 2025
  • Ana fargabar fasinjoji da dama sun rasa rayukansu sakamakon lamarin ciki har sa 'yan gida daya mutum 10

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Ana fargabar wasu fasinjoji da dama sun mutu sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Neja (NSEMA).

Jirgin ruwa ya kife da fasinjoji a Neja
Jirgin ruwa ya gamu da hatsari a Neja Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da harkokin musamman na hukumar, Ibrahim Hussaini, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwa ya yi mummunan hatsari a Taraba, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Neja

Ya bayyana cewa jirgin ruwan, wanda ke ɗauke da adadin da ba a tantance ba na fasinjoji da kaya yana tafiya ne zuwa kasuwar Kwata, Zumba, ya kife ne a tsakiyar kogi.

Ibrahim Hussaini ya bayyana cewa an ceto direban jirgin ruwan tare da wasu fasinjoji kaɗan, inda ɗaya daga cikinsu ke samun kulawa a asibitin gwamnati da ke Kuta.

A cewarsa, ba a iya tabbatar da adadin waɗanda suka rasa rayukansu ba, domin ana ci gaba da aikin ceto da bincike har zuwa lokacin da ake fitar da wannan rahoton.

"Hukumar ta karɓi rahoton hatsarin jirgin ruwa da ya faru a jiya. Jirgin ruwan wanda ke ɗauke da kaya masu yawa da ba a san yawansu ba na fasinjoji da ke hanyarsu ta zuwa kasuwar Kwata Zumba ya kife a kan hanya."

- Ibrahim Hussaini

A cewar hukumar, aikin ceto na gudana ne ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatan NSEMA, masu iyo na gargajiya da kuma masu sa kai daga yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano

Mutane da dama sun rasu

Jaridar Vanguard ta ce basaraken Zumba, Sarkin Ruwa Umar Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce kusan mutum 25 suka rasu.

Ya bayyana cewa wasu mutum 10 daga gida daya na daga cikin wadanda suka mutu, yayin da wasu iyalan suka ce mutanensu biyar sun bace.

Ya kara da cewa ba a san adadin fasinjojim da suka rage ba, domin direban jirgan bai iya fadinsu ba.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Neja
Jirgin ruwa ya gamu da hatsari a Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

A watan Nuwamba na shekarar 2024, mutane akalla 27 sun mutu lokacin da wani jirgin ruwa ya kife a Kogin Neja da ke tsakiyar Najeriya.A watan Nuwamba na shekarar 2024, mutane akalla 27 sun mutu lokacin da wani jirgin ruwa ya kife a Kogin Neja da ke tsakiyar Najeriya.

Jirgin ruwan na ɗauke da kimanin fasinjoji 200 daga jihar Kogi zuwa wata kasuwar kayan abinci da ke jihar Neja, lokacin da ya kife a daren 29 ga watan Nuwamban 2024, inda aka ruwaito cewa fiye da rabin fasinjojin sun bace.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 2 yana jinya, likitoci sun fitar da bayanan lafiyar Gwamna Dikko Radda

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin ruwa ya gamu da mummunan hatsari a jihar Taraban Najeriya.

Hatsarin jirgin ya auku ne a kusa da wata gada wadda ta lalace amma hukumomi suka kasa gyawara.

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin da kayayyaki masu yawa ciki har da motoci suka kife sakamakon hatsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng