Rigima Ta Barke tsakanin Limamai da Ƴan Addinin Gargajiya kan Birne Sarki

Rigima Ta Barke tsakanin Limamai da Ƴan Addinin Gargajiya kan Birne Sarki

  • Kungiyar Limamai da Alarammomi ta Ogun ta nuna damuwa kan hana zirga-zirga da ake shirin kakabawa a Ikolaje da Idiroko saboda jana’izar sarki
  • Limaman sun ce wannan matakin ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma hukuncin kotu da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tun 2017
  • Sun bukaci Gwamna Dapo Abiodun ya sa baki don hana wannan abu, da kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga barazanar rikici da tashe-tashen hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Kungiyar Limamai da Alarammomi ta Jihar Ogun, ta bayyana shiga kafar wando daya yan addinin gargajiya.

Kungiyar ta nuna damuwarta kan shirin masu addinin gargajiya na kafa dokar hana zirga-zirga da rana.

Rigima ta barke tsakanin malamai da yan addinin gargajiya
Limamai sun gargadi ƴan addinin gargajiya kan birne Sarki. Hoto: Oba John Adekunle.
Source: Facebook

Limamai sun kai karar yan gargajiya a Ogun

A cikin wata takarda zuwa ga Gwamna Dapo Abiodun, sun ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma hakkokin dan Adam, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce wannan hana zirga-zirga da rana na da nasaba da bukukuwan jana’izar marigayi Oniko na Iko, Oba John Adekunle, a Ikolaje da Idiroko.

Sun bayyana cewa wannan abu ya sabawa hukuncin kotun jihar da aka yanke a ranar 30 ga Janairu, 2017 a kotun Ipokia.

Hukuncin da aka yanke kan lamarin a baya

Mai shari’a Owoduni ya yanke hukunci cewa dokar hana zirga-zirga da rana haramun ce kuma ya iyakance bukukuwan Oro daga karfe 12 zuwa 4 na safe.

Wasu daga cikin kalamansu sun ce:

“Mun samu sahihan rahotanni cewa wasu mutane sun fara bukukuwan da ke barazana ga zaman lafiya da 'yancin jama'a.”

Sun ce wadannan bukukuwa sun fara tun ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025, kuma za su ci gaba har 19 ga Agusta, 2025.

Sun ce an fara tilasta mutane su rufe shaguna, da hana su yawo, duk da cewa suna gudanar da harkokinsu cikin lumana.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun tarayya ta tunkuɗa ƙeyar ɗan TikTok, G Fresh zuwa gidan kaso

“Duk da muna mutunta addinin gargajiya, ba za mu lamunci tauye ‘yancin dan Adam ba bisa kundin tsarin mulki da dokokin kotu."

- Cewar sanarwar

Malamai sun karar yan addinin gargajiya wurin gwamna
Limamai na neman hana yan addinin gargajiya kusantar masallatansu. Hoto: Prince Dapo Abiodun.
Source: Facebook

Abin da hukuncin ke kunshe da shi

Sun tunatar da Gwamna hukuncin kotu da yarjejeniyar da aka cimma a 2019 da 2020, wacce ta hana bukukuwan Oro su wuce karfe 4 na safe.

Haka kuma sun ce yarjejeniyar ta bukaci ka da a kai bukukuwan Oro kusa da masallatai, makarantu da wuraren ibada.

Sun ce wannan sabawa yarjejeniya da ya faru a 2019 ya kai ga kai farmaki ga masallaci da lakadawa musulmai duka.

Sun kara da cewa shirin tilasta dokar hana fita daga 21 ga Yuli zuwa 19 ga Agusta barazana ce ga zaman lafiya da dokokin kasa.

Rokon da limamai suka yi wa gwamna

Saboda haka, suka roki Gwamna Abiodun ya umurci jami’an tsaro su dakatar da wannan yunkuri tare da kare rayukan jama’a.

Sun bukaci Gwamna ya sake tabbatar da manufar gwamnati da ke hana bukukuwan Oro da rana kamar yadda dokar kotu ta tanada.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso na tsaka mai wuya a siyasa tsakanin shiga APC, PDP ko ADC,'

Sun kuma bukaci a hukunta duk wanda ya saba dokar tare da tabbatar da ‘yancin jama’a na motsi, aiki da ibada ba tare da tsoro ba.

Sojoji sun hana yan gargajiya jana'izar Sarki

Kun ji cewa Sojoji sun hana yan addinin gargajiya shiga jana'izar fitaccen basarake da aka gudanar a bisa tsarin Musulunci.

An birne marigayi Oba Sikiru Adetona, bisa koyarwar Musulunci, inda aka yi masa addu'o’i tare da jagorancin Babban Limamin Ijebu.

Shugabanni da dama ciki har da Aliko Dangote, Yemi Osinbajo da Gwamna Dapo Abiodun sun yaba da jajircewar marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.