"Ku Ankara": NNPP Ta Yi Kira da Babban Murya ga Matasan Arewa kan Kwankwaso

"Ku Ankara": NNPP Ta Yi Kira da Babban Murya ga Matasan Arewa kan Kwankwaso

  • Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta taso tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso a gaba
  • NNPP ta soki tsohon gwamnan na Kano bisa kalaman da ya yi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Jam'iyyar ta shawarci matasan Arewa da ka da su bari Kwankwaso ya yaudare su kan kalaman da yake yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Jam’iyyar NNPP ta ba matasan Arewacin Najeriya shawara kan Rabiu Musa Kwankwaso.

Jam'iyyar NNPP ta shawarci matasan Arewa da su yi watsi da zargin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin tarayya tana nuna wariya ga yankin Arewa, tana mai bayyana hakan a matsayin ƙarya.

NNPP ta ragargaji Rabiu Musa Kwankwaso
NNPP ta shawarci 'yan Arewa kan Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na ƙasa, Dr. Olaposi Ogini, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Legas, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'An buga an bar mu,' Kwankwaso ya faɗi abin da ya sa Kwankwasiyya ta gagara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta kuma soki Kwankwaso, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa zaɓen 2023, bisa yin maganganun da ke ƙoƙarin tayar da ƙura a harkokin siyasa da ƙasa baki ɗaya.

NNPP ta soki Rabiu Kwankwaso

Jam’iyyar ta bayyana ikirarin Kwankwaso cewa gwamnatin tarayya na nuna wariya ga yankin Arewa a matsayin abin da ba shi da tushe, kuma wani shiri ne na ƙirƙiro tashin hankali da gangan.

Idan ba a manta ba dai a cikin 'yan kwanakin nan, Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta ba ta adalci ga Arewa, musamman wajen aiwatar da ayyukan titunan hanyoyi.

Jam’iyyar NNPP ta ce irin waɗannan maganganu daga dattijon kasa abin Allah wadai ne.

"NNPP na kallon wannan zazzafar maganar da Kwankwaso ya yi, yana zargin cewa ana nuna wariya ga Arewa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, da matuƙar damuwa."
"Da irin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yanzu, abin takaici ne sosai ganin tsohon sanata, tsohon minista kuma tsohon gwamna yana furta irin wannan zargi mara tushe, da ya san cewa zai iya tayar da tarzoma a cikin halin da ake ciki."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ballo aiki, kungiyar Yarbawa ta yi masa raddi kan sukar Tinubu

“Muna ganin cewa ba za a yi watsi da irin wannan zargi ba, sai an tilasta masa ya tabbatar da abin da ya fada da hujjoji.”
“Irin waɗannan maganganun sakaci da suka zame masa jiki da kuma aikata wasu abubuwan da suka ci karo da dokokin jam’iyya ne suka kai ga korar Kwankwaso daga NNPP.”

- Olaposi Ogini

NNPP ta yi raga-raga da Rabiu Musa Kwankwaso
NNPP ta caccaki Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

NNPP ta ba matasan Arewa shawara

Jam’iyyar NNPP ta kuma bukaci matasan Arewa da su binciki tarihi da bayanan gwamnati da kansu, su kuma duba irin abin da Kwankwaso ya cimma a lokacin da ya rike madafun iko, daga majalisar dattawa, minista, har zuwa gwamna.

“Arewa kada ta bari Kwankwaso ya yaudare ta da dabarunsa. Ya dace matasa su binciki zargin da ya yi daga bayanan hukumomi da kuma ayyukan da gwamnatin yanzu ta aiwatar."

- Olaposi Ogini

Afenifere ta soki Kwankwaso kan sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi wa Rabiu Musa Kwankwaso raga-raga kan sukar Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

"Labarin ƙarya," An ji gaskiyar abin da ya faru kan batun ganawar Tinubu da Kwankwaso

Kungiyar Afenifere ta bayyana cewa kalaman Kwankwaso ba su dace ba kan zargin cewa Tinubu ya maida Arewa saniyar ware.

Ta bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin tsabagen karya da kuma kokarin tayar da rigima a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel