Wata Sabuwa Ta Ɓullo kan Jinyar da Shugaba Buhari Ya Rika Zuwa Landan kafin Ya Rasu

Wata Sabuwa Ta Ɓullo kan Jinyar da Shugaba Buhari Ya Rika Zuwa Landan kafin Ya Rasu

  • Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa, Garba Shehu ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari na da likitoci a Najeriya
  • Garba Shehu ya saɓawa kalaman Femi Adesina, wanda ya ce da Buhari ya dogara da Najeriya wajen neman magani da ƙila tuni ya rasu
  • A cewar Garba Shehu, yawan zuwan Buhari Landan neman lafiya ra'ayinsa ne kawai amma dai akwai masu duba shi a asibitocin cikin gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Garba Shehu ya ce bai kamata a fassara yawan tafiyar Muhammadu Buhari zuwa ƙasashen waje domin neman lafiya a matsayin raina tsarin lafiyar Najeriya ba.

Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar ya ce Marigayi Buhari yana da likitocin da ke duba lafiyarsa a nan gida Najeriya.

Tsohon mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu.
Garba Shehu ya sabawa Femi Adesina kan jinyar Buhari a Landan Hoto: @GarShehu
Source: Twitter

Garba Shehu ya yi wannan furuci ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Inside Sources na kafar watsa labaran Channels tv.

Kara karanta wannan

'Yadda Buhari ya ki karbar kyautar jirgin sama da aka yi masa', Garba Shehu

Zancen Garba Shehu ya saɓawa kalaman Adesina

Wannan bayani na zuwa ne makonni bayan Femi Adesina, tsohon hadimin Shugaba Buhari ya bayyana cewa da Buhari ya dogara da asibitocin Najeriya, da ya rasu tun daɗewa.

Adesina ya ce Najeriya na da rauni wajen ƙwarewar da ake buƙata don kula da lafiyar Marigayi Shugaba Buhari, rahoton The Cable.

Sai dai Garba Shehu, ya saɓawa waɗannan kalamai na Adesina, inda ya tabbatar da cewa Buhari ya kasance a ƙarƙashin kulawar likitocin Najeriya tun lokacin da yake mulki.

Jinyar Buhari a Landan raina tsarin Najeriya ne?

A cewarsa:

“Ina ganin kuskure ne a ɗauka cewa ya gujewa tsarin lafiyarmu na nan cikin gida. Yana da likita ɗan Najeriya babban likitan da ke kula da lafiyarsa kai tsaye.
"Haka kuma yana zuwa asibitin fadar gwamnati wanda wani likita mashahuri mai gogewa ke jagoranta.”

Garba Shehu ya ce tawagar likitocin da ke kula da Muhammadu Buhari sun kasance a shirye ko yaushe don yin duk abin da ya kamata na kiwon lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

“A duk lokacin da ya buƙaci kulawar lafiya cikin gaggawa, su ne ke duba shi a nan Najeriya,” inji shi.
Marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Garba Shehu ya ce Buhari ya ci gaba da zuwa Landan neman lafiya ne bisa ra'ayin kansa Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Meyasa Buhari ya fi yarda ya tafi asibitin Landan?

Ya amince da cewa Buhari ya saba da tafiya ƙetare musamman Landan don jinyar kansa, amma ya ce hakan ya ta'allaka ne da zaɓin kashin kansa.

“Game da yadda ya tsaya kan dabi’arsa ta zuwa neman magani a ƙetare, hakan ra’ayinsa ne. Ba wai ya raina harkar lafiyar Najeriya ba ne, ko yana ganin babu ƙwarewa.”
“Mutane da yawa da ke zuwa ƙetare suna ganin likita kamar yadda na taɓa gani a Amurka, za ka shiga ofishin likita ka tarar likitan Bafillace ne ko kuma ɗan Najeriya,” inji shi.

Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu a ranar 13 ga Yuli 2025 a wani asibiti da ke Landan bayan fama da doguwar jinya.

Shugaban Gambia ya je ta'aziyyar Buhari a Daura

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Buhari, Sheikh Abubakar Gumi da wasu jagororin Najeriya 5 da suka rasu a birnin Landan

Shugaba Barrow ya isa Daura ne a ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025 domin jajantawa iyalan marigayi Buhari kan babban rashin da suka yi.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, da wasu manyan jami’ai ne suka tarbe su a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'adua.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262