Daniel Bwala Ya Kwatanta Lafiyar Tinubu da Ta Sauran Shugabannin Najeriya
- Hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan lafiyar ubangidansa bayan ya sha tambayoyi
- Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da isashshiyar lafiya fiye da sauran wasu shugabanni
- Hadimin shugaban ƙasan ya bayyana cewa Tinubu ya samu nasarori masu yawa a cikin shekara biyu da ya yi a kan mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya yi magana kan lafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da lafiya fiye da yawancin shugabanni a ƙasashen da suka ci gaba.

Source: Twitter
Hadimin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar DW Africa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin hirar, Daniel Bwala ya ba da amsar tambayoyi kan yawan tafiye-tafiyen zuwa jinya da Tinubu ke yi zuwa ƙasashen waje da kuma goyon bayan da yake samu tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya maganar lafiyar Shugaba Tinubu?
"A gaskiya, shugaban Najeriya yana da lafiya da ƙwarin jiki fiye da yawancin shugabannin ƙasashen da suka ci gaba."
- Daniel Bwala
Da aka tambaye shi ko goyon bayan da Tinubu ke samu da wuri wani salo ne na ƙarfafa mulki, Bwala ya ce hakan na cikin tsarin APC.
"Tsari ne a jam’iyyarmu cewa bayan rabin wa’adin mulki, za a auna a sikeli a ga abin da mutum ya yi."
"Don haka ba wai Shugaba Bola ne kaɗai ba. Duk wanda ke kan mulki a lokacin, bayan kammala rabin wa’adin mulki, za a tantance domin ganin ko ya cancanci a ba shi dama ya ci gaba."
- Daniel Bwala
Ya ce Shugaba Tinubu ya samu nasarar wuce wannan tantancewa da gagarumin maki.
“Mun auna, mun ga cewa ya yi aiki ƙwarai da gaske. Don haka muna da cikakken tabbaci a kan 2027 cewa muna da goyon bayan jama’a."
- Daniel Bwala
Waɗanne nasarori Tinubu ya samu?
Da aka nemi ya bayyana wasu daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Tinubu, Bwala ya ce samar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi na daga cikin manyan ci gaban da gwamnatinsa ta samu.

Source: Twitter
"Ƙarfafa dimokuraɗiyya na ɗaya daga ciki, wato bayar da ƴancin kai ga ƙananan hukumomi."
"Ƴancin kai wanda ke ba shugabannin ƙananan hukumomi damar sarrafa manyan kuɗaɗe."
- Daniel Bwala
Ya ƙara da cewa yanzu haka gwamnatocin jihohi na iya ɗaukar jami’an sa-kai, sayen motoci da kayan aiki da suka dace don aikin sa-ido da tattara bayanan leƙen asiri da kuma tabbatar da doka da oda.
Daniel Bwala ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta inganta fannin lafiya da samun abinci ga talakawa a faɗin ƙasar nan.
An taso Kwankwaso a gaba kan sukar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi wa Rabiu Musa Kwankwaso, raddi kan sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
"An yi watsi da Arewa," Kwankwaso ya soki Gwamnatin Tinubu, ya faɗi kalamai masu daci
Ƙungiyar Afenifere ta caccaki Kwankwaso inda ta zarge da ƙoƙarin tada rigima tsakanin yankin Kudu da na Arewa.
Ta bayyana a matsayinsa na wanda ya taɓa yin gwamna kuma yake tsohon minista, bai kamata irin waɗannan kalaman su fito daga bakinsa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

