Dakarun Sojoji Sun Yi Rugu Rugu da 'Yan Ta'adda, an Tura Miyagu da Dama Barzahu
- Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana nasarorin da dakarunta suka samu a kan ƴan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan
- Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa bayan sun yi musayar wuta mai zafi da su
- Hakazalika, sun kuma ƙwato makamai da kayayyaki masu yawa daga hannun miyagun ƴan ta'addan masu tayar da ƙayar baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar kashe ƴan ta’adda da dama.
Rundunar sojojin ta kuma bayyana cewa an cafke wasu ƴan ta'addan a jerin hare-haren da aka tsara bisa bayanan sirri a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan riƙo ta hulɗa da jama’a ta rundunar sojoji, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta fitar a ranar Asabar a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan
Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
Anele ta ce daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Yulin 2025, sojoji sun kashe ƴan ta’adda bakwai, sun kama mutane 10 da ake zargi da aikata laifuka.
Ta ce sojojin sun kuma karɓi mutane 19 daga cikin iyalan ƴan ta’adda da suka miƙa wuya, tare da ƙwato makamai da alburusai da kayan aikin yaƙi daga fagen fama daban-daban, rahoton Peoples Gazette ya tabbatar.
A jihar Borno, ta bayyana cewa dakarun Bataliya ta 151 Task Force sun yi wa wasu ƴan ta’addan ISWAP/JAS kwanton ɓauna a ƙauyen Bula Daburu, inda suka kashe guda biyu tare da ƙwato kayayyaki da suka haɗa da keke guda takwas, buhunan abinci da tabarmi.
Anele ta kuma ce dakarun Bataliya ta 222 sun kashe wani ɗan ta’adda yayin wani kwanton bauna a kusa da madatsar ruwa ta Alau da ke ƙaramar hukumar Konduga.
Ta ƙara da cewa iyalan ƴan ta’adda 19 da suka haɗa da mata bakwai da yara 12 sun miƙa wuya ga Bataliya ta 202 da ke Bama, inda suka bayyana cewa ba za su iya jure rayuwa a sansanonin ƴan ta’adda ba.
"A jihar Neja, dakarun Operation Fansan Yanma tare da haɗin gwiwar rundunar sama, sun kashe ƴan ta’adda da dama a ƙauyen Mahula, inda suka ƙwato bindigogi AK-47 guda biyu, babura 18 da harsasai."
“A Zamfara, dakaru sun kashe ƴan ta’adda uku a ƙaramar hukumar Maradun, inda suka ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu, babura da na’urorin sadarwa."
"An lalata babura guda takwas a ƙaramar hukumar Anka, sannan aka ƙwato dabbobin da aka sace har guda 78, kuma aka miƙa su ga hukumomin da suka dace."
- Laftanal Kanal Appolonia Anele
Sojoji sun cafke wadanda ake zargi
A jihar Plateau, Anele ta bayyana cewa dakarun Operation Safe Haven sun kama wasu manyan mutane da ake zargi da hannu a kashe-kashe, garkuwa da mutane da hare-hare kan jami’an tsaro, ciki har da Dayabu Idris da Ardo Forof Ardo Habibu Mohammed.

Source: Twitter
Ta ƙara da cewa dakarun sun ƙwato bindigar AK-47, harsasai, sannan suka kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wani makiyayi a ƙaramar hukumar Jos ta Gabas.
“A wani wuri daban, dakarun Operation Whirl Stroke a jihar Benue sun kashe wani mai garkuwa da mutane tare da ceto mutane uku a garin Gbise."
“A jihar Enugu, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a dajin Akwuke, inda kuma wani daga cikinsu ya rasa ransa bayan an ƙara kai wani samame, sannan aka lalata mafakarsu."
- Laftanal Kanal Appolonia Anele
Sojoji sun hallaka jagoran ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka jagoran ƴan bindiga a jihar Sokoto.
Sojojin sun hallaka ɗan bindigan mai suna Dan Dari Biyar ne a yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Jami'an tsaron sun hallaka jagoran ƴan bindigan ne lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa na mutanen da ya sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

