Jirgin Ruwa Ya Yi Mummunan Hatsari a Taraba, an Samu Asarar Rayuka

Jirgin Ruwa Ya Yi Mummunan Hatsari a Taraba, an Samu Asarar Rayuka

  • An samu hatsarin jirgin ruwa bayan ya ɗauko fasinjoji da motoci a jihar Taraba
  • Hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a ƙaramar hukumar Gassol ya yi sanadiyyar asarar rayuka tare da ta dukiyoyi bayan ya kife a cikin kogi
  • Jirgin ruwan dai ya kife ne a kusa da wata gada wadda ta ɓalle a shekarar da ta gabata kuma har yanzu hukumomi sun kasa gyarawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Wani jirgin ruwa ya gamu da hatsari bayan ya kife kusa da gadar Namnai da ta lalace a yankin ƙaramar hukumar Gassol a jihar Taraba.

Hatsarin jirgin ruwan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku har lahira.

Jirgin ruwa ya gamu da hatsari a Taraba
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Taraba, fasinjoji sun mutu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:20 na dare a ranar Juma’a, 25 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji sun daƙile mugun shirin ƴan ta'adda, sun kashe mai ɗaukar bidiyo domin yaɗa ƙarya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Taraba

Lamarin ya auku ne lokacin da wani jirgin ruwa da ke ɗauke da fasinjoji da motoci ya kife a cikin ruwan yayin da yake tsallaka Kogin Namnai a kan hanyar Jalingo zuwa Wukari a Taraba.

Shugaban ƙungiyar masu sufurin jirgin ruwa a jihar Taraba, Jidda Mayoreniyo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa mutane uku sun mutu a hatsarin, yayin da aka ceto wasu da dama.

Hakazalika sama da motoci huɗu da ke cikin jirgin lokacin hatsarin na cikin ruwan har yanzu, kuma fasinjoji da dama sun rasa kayansu da sauran dukiyoyinsu.

Gadar Namnai, wacce da can ke zama muhimmin wurin haɗa Taraba da Benue da sauran yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, ta ɓalle ne a watan Satumba na bara, kuma har yanzu ba a gyara ta ba.

Rahotanni sun bayyana cewa fiye da fasinjoji 4,000 da ɗaruruwan motocci ake jigilar su a kullum a kan Kogin Namnai tun bayan ɓallewar gadar.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 2 yana jinya, likitoci sun fitar da bayanan lafiyar Gwamna Dikko Radda

Bincike ya kuma nuna cewa fiye da motoci 50 sun faɗa cikin kogin yayin da ake ƙoƙarin jigilar su a jirgin ruwa.

Jirgin ruwa ya gamu da hatsari a Taraba
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Taraba Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan hatsarin jirgi

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a jihar Kebbi.

Hatsarin jirgin ruwan dai ya auku ne a kogin Yauri da ke Kebbi, inda ya yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutane hudu har lahira.

Mutanen dai sun rasu ne bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya nutse a cikin kogin. An kuma nemi wasu fasinjoji an rasa bayan sun yi ɓatan dabo a ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng