Babbar Magana: An Yi Barazanar Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN

Babbar Magana: An Yi Barazanar Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN

  • Majalisar Wakilai ta yi barazanar bayar da sammacin kama gwamnan CBN, Olayemi Cardoso bisa zargin raini da rashin mutuntata
  • Kwamitocin Majalisa kan binciken kasafin kudi da kadarorin gwamnati ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar yau Juma'a
  • Sun ce gwamnan CBN ya take umarnin da aka basa kan kuɗin asusun da aka daina amfani da su kuma ya ki amsa gayyatar da aka tura masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kwamitocin Majalisar Wakilai kan binciken lissafin kudi da kadarorin gwamnati sun yi barazanar bayar da sammacin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso.

Sun yi wannan baranaza ne saboda kin amsa gayyata sau da dama da kuma gazawar bin dokoki da kudurori da suka shafi Dokar Alhakin Kudin Kasa ta 2007 da Dokar Kudi ta 2020.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso na tsaka mai wuya a siyasa tsakanin shiga APC, PDP ko ADC,'

Gwamnan babban banki CBN, Cardoso.
Majalisa ts yi barazanar ba da umarnin kamo gwamnan CBN, Cardoso Hoto: @CentBank
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwar haɗin gwiwa da kwamitocin biyu suka fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin kwamitocin, Hon. Bamidele Salam (Binciken Lissafin Kudi) da Hon. Ademorin Kuye (Kadarorin Gwamnati), sun bayyana cewa babu wata mafita illa su sa a kamo gwamnan CBN.

Meyasa aka yi wa gwamnan CBN barazana?

Sun ce za su sa a kamo Cardoso ne saboda raini da wulakancin da suke zargin Gwamnan CBN yana yi wa umarnin majalisar wakilai ta kaasa.

A cewarsu, Akanta Janar na Tarayya ya bada rahoton cewa gwamnati na bin CBN bashin rarar kudin aiki har Naira tiriliyan 5.2 tsakanin 2016 da 2022.

Hukumar kula da harkokin kasafin kudin ƙasa ta tabbatar da wannan rahoto a wani takaitaccen bayani da ta mikawa Majalisar Dokoki.

'Yan majalisar sun kafa hujja da Dokar Kudi ta 2020 wadda ta tanadi cewa duk ribar hannun jari da aka bari sama shekaru shida, tare da kudin asusun bankuna da aka daina amfani da su, a tura cikin asusu na musamman.

Kara karanta wannan

Cacar baki ta kaure tsakanin Akpabio da Barau da aka zo tantance wani tsohon sanata

Wannan asusu dai ministan kudi da harkokin tattalin arziki ne ke jagorantar kwamitin da ake kula da shi.

Umarnin Majalisa da gwamnan CBN ya take

Kwamitocin sun umurci CBN da ya biya Gwamnatin Tarayya Naira tiriliyan 3.64 wato kashi 70% na rarar kudin aiki daga cikin tiriliyan 5.2 cikin kwana 14.

Haka kuma, sun umurci babban bankin da ya bayar da alƙaluman kudin hannun jari da kudaden asusun da aka daina amfani da su kafin ranar 30 ga Yuni, 2025.

Majalisar Wakilai ta fusata da gwamnan CBN.
Majalisar Wakilai ta ce gwamnan CBN ya raina umarninta Hoto: @CentBank
Source: Twitter

Sannan an umarci CBN ya tura waɗannan kudi zuwa asusu na musamman da ke tara kuɗin da jama'a ba su karɓa ba cikin mako biyu bayan samun sakon Majalisa.

Duk da haka, sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan CBN ya kasa mutunta wannan kuduri kuma ya gaza bayyana gaban kwamitin don bayar da dalilin faruwar hakan.

'Yan majalisar sun jaddada cewa matakan da suke dauka suna kan tsarin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, don haka suna iya ba da umarnin kama gwamnan CBN, rahoton Punch.

Majalisar Wakilai ta tafi hutun watanni 2

Kara karanta wannan

Zamfara: An shiga tashin hankali bayan samun gawar malamin Musulunci a mugun yanayi

A wani labarin, kun ji cewa bayan kammala zaman ranar Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025, Majalisar Wakilai ta tafi hutuɓna tsawon watanni biyu.

Majalisar za ta koma aikinta a ranar 23 ga Satumba 2025, tare da ci gaba da nazari da amincewa da kudurori da sauran batutuwan da ke gabanta.

Kakakin Majalisar ya bayyana cewa hutun ba kawai hutu ne na jiki ba, dama ce ga ‘yan majalisa su koma mazabunsu domin ƙara kusantar da kansu ga al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262