An Sanya Lokacin da Za a Yi Jana'izar Marigayi Sarkin Gusau, Mai Martaba Ibrahim Bello
- Za a yi sallar jana'izar Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, da ƙarfe 2:30 na rana a babban Masallacin Juma'a na birnin Gusau
- Shugaban ƙaramar hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam ya tabbatar da cewa za a birne marigayin bayan kammala Sallar Juma'a
- Marigayi Sarki Ibrahim Bello ya rasu da safiyar Juma'a a Abuja yana da shekaru 71 bayan doguwar rashin lafiya a wani asibitin Abuja
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhini bisa rasuwar sarkin Gusau, yana mai cewa za a tuna da sarkin saboda shugabancinsa na gari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara – Za a gudanar da sallar Jana’iza ga marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, da misalin karfe 2:30 na rana a babban masallacin Juma’a na Gusau.
Shugaban karamar hukumar Gusau, Alhaji Abubakar Imam, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce za a binne gawar marigayin bayan kammala Sallar Juma’a.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto Alhaji Abubakar Imam yana cewa:
“Ina so in sanar da al’ummar Musulmi a jihar nan da ma fadin kasar nan cewa Allah maɗaukakin sarki, wanda ke da iko a kan komai, ya karɓi rayuwar Mai Martaba Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello.
“Za a gudanar da jana’izarsa yau, 25 ga watan Yulin 2025 bayan Sallar Juma’a a masallacin Juma’ar fadar Sarkin Gusau.
“Allah ya gafarta masa, ya jikansa, ya kara masa rahama, kuma ya sake haɗa mu a Aljanna. Ameen.”
Mun ruwaito cewa marigayin sarkin ya rasu da safiyar Juma’a a wani asibiti da ke Abuja bayan fama da doguwar rashin lafiya, yana da shekaru 71 a duniya.
Tinubu ya yi ta'aziyyar Sarkin Gusau
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar Dakta Ibrahim Bello, Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar da sanarwa a shafin ma'aikatar watsa labarai na X, cewa Sarki Ibrahim ya rasu ranar Juma'a da safe a Abuja, yana da shekaru 71.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya fitar da bayanai da mutane ke son sani kan rasuwar Sarkin Gusau
Sanarwar Onanuga ta ce:
"Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar sarkin gargajiyar a matsayin babban rashi ga kowa ba kawai ga yankinsa ba, yana mai tunawa da hidimar da ya yi a matakai daban-daban.
"Shugaban ya ce za a tuna da marigayi Sarki Ibrahim saboda jajircewarsa a aiki, sadaukarwarsa ga mutanensa da kuma shugabanci na gari."
Shugaba Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnati, al'ummar jihar Zamfara, da kuma iyalan marigayi sarkin.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Abubuwan da za a sani kan Sarkin Gusau
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, ya rasu yana da shekara 71 a duniya bayan fama da doguwar rashin lafiya a Abuja.
Binciken da Legit.ng ta gudanar ya bayyana cewa marigayin ya hau karagar mulki a shekarar 2015, bayan dogon aiki a fannoni da dama na gwamnati.
Kafin zama Sarki, Dr. Ibrahim Bello ya rike mukamai masu muhimmanci a masarautar Gusau, ciki har da Kwamishina, Darakta-Janar da kuma Sakatare.
Asali: Legit.ng
