An Tare Motar 'Yan Kasuwa a Filato an Kashe Mutane, Mata da Yara Sun Mutu
- Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara sun kai hari kan mata da yara a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar a yankin Bokkos
- Harin ya auku a kan titin Chirang da ke yankin Mangor, inda mutum akalla 14 suka mutu a sakamakon harbin bindiga
- Har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin Jihar Filato ko ’yan sanda dangane da wannan mummunan hari da aka kai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Akalla mutum 14, ciki har da mata da yara kanana, sun rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a karamar hukumar Bokkos ta Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a hanyar Chirang da ke cikin yankin Mangor, inda aka ce maharan sun bude wuta kan fasinjojin da ke dawowa daga kasuwa.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta yi hira da wasu mutane a yankin, inda suka nuna damuwa kan abin da ya faru da matafiyan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin na zuwa kasa da wata guda bayan wasu matafiya daga Jihar Kaduna da ke kan hanyarsu ta zuwa daurin aure, suka gamu da ajalinsu a hannun wasu matasa a jihar Filato.
An kashe 'yan kasuwa a hanyar Filato
Rahotanni sun ce wadanda lamarin ya rutsa da suna dawowa ne daga kasuwar da ake ci a garin Bokkos duk ranar Alhamis, lokacin da aka yi musu kwanton-bauna.
Maharan sun fito ne daga daji inda suka tare hanya suka fara harba bindiga ba tare da kakkautawa ba, wanda hakan ya janyo mutuwar mutane da dama da raunata wasu.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa harbin ya tsananta sosai, kuma da kyar wasu suka tsere.
Kungiyar al’ummar Bokkos ta yi martani
Kungiyar cigaban al’ummar Bokkos (BCDF), ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana bakin cikinta dangane da aukuwar wannan hari da ya sake jefa al’umma cikin firgici da jimami.

Kara karanta wannan
Zamfara: An shiga tashin hankali bayan samun gawar malamin Musulunci a mugun yanayi
Shugaban kungiyar, Farmasum Fuddang, ya ce wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da ake kokarin sasanta rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Ya ce:
“Muna cikin zaman lafiya da hadin kai, amma hakan bai hana wasu bata-gari kai hari ba.”

Source: Twitter
Kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su dauki mataki cikin gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman ganin yadda hare-hare ke karuwa.
A lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga gwamnatin Jihar Filato ko rundunar ’yan sandan jihar game da harin, duk da cewa lamarin ya dauki hankalin al’ummar yankin.
An kama masu garkuwa a Kwara da Kogi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi ta sanar da cafke wasu mutane 13 da ake zargi suna garkuwa da mutane.
Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen ne bayan gwabza fada da jami'an tsaro a tsakanin jihohin Kogi da Kwara.
Baya ga haka, an cafke wani mutum da ake zarfi yana cikin mutanen da ke taimaka wa 'yan bindiga wajen tattara bayanan mutane.
Asali: Legit.ng
