Tsadar Rayuwa: Shugaba Tinubu Ya Fara Gano Gaskiya, Ya Aika Sako ga Gwamnonin APC
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da babbar murya ga gwamnonin APC kan halin da ake ciki a ƙasa
- Tinubu ya buƙaci gwamnonin na APC kan su ƙara ƙaimi wajen inganta rayuwar mutanen da suke ƙarƙashinsu
- Shugaban ƙasan ya nuna cewa wasu ƴan Najeriya sun fara ƙorafi kan yadda abubuwa suke tafiya a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi hannunka mai sanda ga gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnonin na APC da su ninka ƙoƙarinsu wajen kawo ci gaba ga mutanen da ke ƙarƙashinsu.

Asali: Twitter
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) karo na 14 na jam’iyyar APC da aka gudanar a Banquet Hall na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Bola Tinubu ya ba da?
Ya yi gargaɗin cewa har yanzu ƴan Najeriya da dama ba su gamsu da yadda ake tafiyar da mulki da sanin amfanin romon dimokuraɗiyya ba, rahoton Vanguard ya tabbatar da wannan.
Shugaba Tinubu ya buƙaci shugabannin jam’iyya da ƴan siyasa da aka zaɓa da su sake kusantar jama’a tare da ƙara himma wajen kyautata rayuwar al’umma a matakin ƙasa.
“Muna bukatar mu ƙara aiki. Ƴan Najeriya har yanzu suna korafi a matakin ƙasa."
"Ku gwamnoni, dole ne ku jiƙa ƙasa da ayyuka tare da kawo ƙarin amfanin dimokuraɗiyya a ƙananan hukumomi. Ba za mu zauna muna hutawa ba. Dole ne mutanenmu su ji tasirin gwamnati kai tsaye."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu na son haɗin kan APC?
Ya jaddada cewa ƙarfin jam’iyyar APC da makomarta na dogara ne da irin rawar da take takawa a matakin ƙasa, inda jama’a ke mu’amala kai tsaye da manufofi da ayyukan gwamnati.
Shugaban ƙasar ya kuma yaba da yawan ƙuri'un amincewa da aka ba shi daga shugabannin jam’iyya a faɗin ƙasa.
Ya ce irin wannan goyon baya dole ne a mayar da shi zuwa cikakken aiki, haɗin kai, da tsayuwa tsayin daka a matakai daban-daban na gwamnati.
"Na karɓi ƙuri’ar amincewa da aka nuna mani a yau da kuma wacce aka nuna a matakin jihohi. Amma yanzu dole ne mu sauya wannan amana zuwa aiki. Dole ne mu ƙarfafa rassanmu na jam’iyya tare da gina haɗin kai a cikin jam’iyya."
- Shugaba Bola Tinubu

Asali: Twitter
Shugaba Tinubu ya bayyana shirinsa na gina sabuwar hedkwatar jam’iyyar APC a Abuja, yana cewa gidan Muhammadu Buhari da ake amfani da shi a yanzu ya yi kaɗan wajen biyan buƙatun jam’iyyar na yanzu da na gaba.
Hashim Usman ya yaba kan yadda shugaban kasan ya fito ya gayawa gwamnoni ya kamata su kara zage damtse.
"Ana ta cewa jihohi sun kara samun kudade daga gwamnatin tarayya amma talaka baya ganin amfanin hakan."
"Ya kamata gwamnoni su kara zage damtse wajen inganta rayuwar talakawa musamman wadanda suke zaune a yankunan karkara."
- Hashim Usman
HSS
Tinubu ya taso ƴan haɗaka a gabaubu ya taso ƴan haɗaka a gaba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi shaguɓe ga ƴan haɗaka da ke ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Shugaba Tinubu ya yi watsi da haɗuwar ƴan adawan a wuri guda, inda ya bayyana su a matsayin ruɗaɗɗu.
Mai girma Bola Tinubu ya kuma buɗe ƙofa ga duk ƴan siyasan da suke son shigowa cikin jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng