Bayan Ganawa da Tinubu, An Hangi Kwankwaso a Wurin Taro Tare da Gwamna Abba da Sarkin Kano
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Kwankwaso ya halarci taron masu ruwa da tsaki kan gyaran kundin tsarin mulki
- Taron wanda ya gudana a gidan gwamnatin Kano, ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II
- Gwamnatin Kano ta ce an shirya taron domin jihar ta ɗauki matsaya gabanin taron jin ra'ayoyin jama'a na Majalisar Dattawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf sun halarci taron tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya.
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya halarci taron wanda ke gudana a ɗakin taron da ke cikin fadar gwamnatin Kano yau Alhamis.

Source: Twitter
Tun farko dai gwamnatin Kano ta gayyaci duka masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin fararen hula da sauran al'umma zuwa wurin wannan taro, a wata sanarwa da ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano
Sanarwar wacce mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce za a fara taron ne da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar rana yau Alhami.
Gwamnatin ta gayyaci al'umma zuwa taron
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa wannan dama ce da jama'a za su ba da gudummuwa tare da bayyana ra'ayoyinsu gabanin taron jin ra'ayoyin jama'a na Majalisar Dattawa.
Sanarwar ta miƙa sakon gayyata ga dukkan ƴan jihar Kano kama daga masu ruwa da tsaki, shugabanni, ƴan kasuwa, sarakuna da duk wani mai kishin ƙasa.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnatin Kano na gayyatar al'umma zuwa taron masu ruwa da tsaki dangane da gyaran kundin tsarin mulkin kasa domin samar da matsayar jihar kafin zaman jin ra'ayin jama'a da za a gudanar a Majalisar Dattawa.
"Ana gayyatar duka masu ruwa da tsaki, ciki har da 'Yan Majalisar Dokoki na Jiha da na Tarayya, kungiyoyin fararen hula, kafafen yada labarai, 'yan kasuwa, sarakuna, malamai, da kungiyoyin kwadago da ƴan kasuwa.

Kara karanta wannan
"An yi watsi da Arewa," Kwankwaso ya soki Gwamnatin Tinubu, ya faɗi kalamai masu daci
"Duka masu rike da mukamai karkashin gwamnatin Kano, da tsofaffin gwamnoni ana sa ran za su halarci wannan muhimmiyar tattaunawa da aka shirya yi ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025 da ƙarfe 1:00 na rana."

Source: Twitter
Kwankwaso, Abba da Sanusi II sun halarta
Bayan fara taron yau Alhamis a fadar gwamnatin Kano, an ga Kwankwaso, Gwamna Abba da Sarki Sanusi II a zaune a wuraren da aka tanada masu a ɗakin taron.
Taron mai taken: “Zo mu tattauna don kawo sauyi” ya samu halartar jami’an gwamnati, kungiyoyin fararen hula, da sauran masu ruwa da tsaki a cewar rahoton Daily Trust.
Kwankwaso ya gana da Tinubu a Aso Rock
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso a fadarsa da ke Abuja.
Ganawar na zuwa ne jim kadan bayan da Kwankwaso ya halarci taron tattalin arzikin daji da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa.
Rabiu Kwankwaso ya ce ya tattauna da shugaba Tinubu kan batutuwan da suka shafi siyasa, inda ya bayyana yiwuwar yin aiki tare.
Asali: Legit.ng