Tsohuwar Matar Kwamishina Ta Kwance Masa Zani a Kasuwa, Ta Roki Gwamna Bago Alfarma

Tsohuwar Matar Kwamishina Ta Kwance Masa Zani a Kasuwa, Ta Roki Gwamna Bago Alfarma

  • Tsohuwar matar kwamishina a jihar Niger ta taso shi a gaba kan zargin cin zarafi da barazana da yake yi mata
  • Hadiza Ali-Musa ta zargi tsohon mijinta, kwamishinan muhalli, Yakubu Kolo, da barazana da tsoratarwa bayan sun rabu
  • Hadiza ta ce aurensu na shekara tara ya cika da cin zarafi, yanzu kuma yana kokarin hana ta kula da ‘ya’yanta biyu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Tsohuwar matar kwamishina a jihar Niger ta zarge shi da yi mata barazana bayan sun rabu a kotu.

Hadiza Ali-Musa tana zargin kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Niger, Yakubu M. Kolo da cin zarafinta.

Ana zargin kwamishina da jin zarafin tsohuwar matarsa
Tsohuwar matar kwamishina a Niger ta zarge shi da cin zarafi. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Facebook

Ana zargin Kwamishina da cin zarafin tsohuwar matarsa

Da take magana da Daily Nigerian a ranar Laraba a Abuja, Hadiza Ali-Musa ta ce tsohon mijinta ya sha kokarin hana ta hakkinta.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yi zarra, Abba ya ƙara samun lambar gwarzon gwamnoni a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohuwar matar kwamishinan ta koka kan barazana da tsoratarwa daga wurin tsohon mijinta wanda ake cigaba da yi mata har yanzu.

Ta ce yana kokarin hana ta mallakar yaransu biyu, har da tsare-ta da ‘yan sanda suka yi.

Matar ta zargi kwamishina da cin zarafinta

Uwar yara biyu ‘yar shekara 38 ta koka cewa aurensu na shekara tara ya kasance mai cike da cin zarafi da wahala.

Ta ce:

“Na sha wahala a hannunsa, sai da na garzaya kotu don samun saki daga wurin wannan mutumin. Yanzu kuma yana ta neman hana ni zaman lafiya.
“Ina rayuwa cikin fargaba. Ban san me zai faru da ni ko nan da mintuna ba gaskiya. Ina matukar son in kasance nesa da shi.
“Tun farkon shekarar nan ya turo ‘yan sanda domin kama ni saboda kawai ya fahimci ba zan mika masa yaran ba.”
An roki gwamna alfarma kan zargin kwamishinsa
Ana zargin kwamishina da cin zarafin matarsa a Niger. Hoto: Legit.
Source: Original

Rokon da matar ta yi ga Gwamna Bago

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun dimauce da aka kai musu hari da dare, an sace shanu

Hadiza Ali-Musa ta roki Gwamna Umaru Bago da Kwamishinan ‘Yan sanda na Niger su shiga lamarin domin hana tsohon mijinta ci gaba da barazanar rayuwarta.

Da aka tuntubi Kwamishinan don jin ta bakinsa, ya karyata zargin da tsohuwar matarsa ke yi inda ya ce ba zai ce komai kan lamarin ba.

Ya ce ita ce ta garzaya kotu kan abin da ke faruwa duk da kokarin da iyayenta suka yi kan lamarin da ke faruwa.

Ya ce:

“Yaya? Ita ce ta garzaya kotu duk da kokarin da iyayenta suka yi. Don haka ba zan ce komai ba tun da batun na gaban kotu ne.”

An zargi Kwamishina da sace yarsa a Bauchi

A baya, mun ba ku labarin cewa kwamishinan Ruwa a jihar Bauchi, Abdulrazak Nuhu Zaki, ya musanta zargin satar yarinya, yana mai cewa Zainab diyarsa ce ta jini kuma yana da hakki a kanta.

Zaki ya bayyana cewa ya rabu da mahaifiyarta ne saboda matsin lamba daga danginta, duk da kokarin wasu wajen daidaita rikicin auren domin samun maslaha.

Ya ce kotuna uku sun yanke hukunci a kansa, amma ana hana shi ganin diyarsa, har sai da ta yanke shawarar komawa wajensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.