Majalisa Ta Mika Bukata ga Tinubu, Ta Nemi a Girmama Marigayi Dantata

Majalisa Ta Mika Bukata ga Tinubu, Ta Nemi a Girmama Marigayi Dantata

  • Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta girmama marigayi Aminu Dantata ta hanyar sanya sunansa a wani katafaren gini
  • Sanata Barau I. Jibrin da wasu daga cikin 'yan majalisar Kano ne suka mika kudirin saboda gudunmawar da Alhaji Dantata ya bayar ga 'kasa
  • Ya ce Dantata ya tallafa wajen gina makarantu, masallatai da cibiyoyin lafiya ta hannun gidauniyarsa a sassa daban-daban na Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoMajalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta girmama marigayi dattijon kasa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

A zaman da majalisar ta yi a ranar Talata, an bukaci gwamnatin ta yi hakan ta hanyar sanya sunansa a wani muhimmin gini ko wurin tarihi na kasa.

Sanata Barau I Jibrin
Sanata Barau Jibrin ya jagoranci mika kudirin girmama Dantata Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wani bidiyo da mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta nuna yatsa ga majalisa bayan an hana ta shiga

'Yan majalisar dattawa sun bijiro da kudiri

Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, tare da Sanata Rufai Hanga da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ne suka gabatar da kudirin.

Alhaji Dantata, dattijon kasa wanda aka san shi da taimakon jama'a da addini da kuma sadaukarwa ga cigaban al’umma da kasa, ya rasu a ranar 28 ga Yuni 2025, yana da shekaru 94 a duniya.

A lokacin da yake gabatar da kudirin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ya bayyana rayuwar Alhaji Dantata a matsayin abin koyi da kuma abin alfahari.

Ya kara da bayyana cewa tarihi ba zai taba manta wa da gagarumar gudunmawar da ya bayar a fannonin kasar nan daban-daban ba.

Majalisa ta yabi Marigayi Aminu Dantata

Sanata Barau ya bayyana cewa marigayi Dantata ya shahara da tawali’u, kishin addini, bayar da taimako da kuma kokarin ganin an samu cigaba a cikin al’umma da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta yi raddi mai zafi ga Akpabio kan hana ta shiga majalisa

Sanata Barau ya kara da cewa Alhaji Dantata tallafa wajen gina makarantu, masallatai da cibiyoyin lafiya a Arewacin Najeriya da ma wajenta.

Ya ce:

“Ya sadaukar da dukiyarsa wajen taimakon jama’a. Ta hannun gidauniyarsa da kuma kashin kansa, ya dauki nauyin gina makarantu, masallatai, cibiyoyin lafiya da shirye-shiryen jin kai a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya da ma wajenta.

Sanata Barau I Jibrin ya kara da bayyana cewa rayuwar Alhaji Dantata ya yi tasiri wajen sauya rayuwar jama'a, kuma ba za a manta da shi ba.

Majalisa ta waiwayi ma'aikatan kasar nan

A baya, mun wallafa cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta fara duba wani kuduri da ke neman hana wa ma’aikatan gwamnati da masu rike da madafun iko da iyalansu zuwa makarantun kudi.

Haka kuma 'kudirin yana neman a hana su sanya yaransu da karan kansu zuwa asibitocin kudi a ciki da wajen Najeriya saboda inganta cibiyoyin gwamnati a fadin kasar nan.

'Dan majalisar wakilai daga jihar Abia, Hon. Amobi Ogah, ne ya dauki nauyin wannan kuduri, wanda yanzu haka ya tsallake karatun farko a zaman majalisar ranar Talata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng