Gudumar Majalisa Za Ta Hau Manyan Gwamnati, Za a Hana Su zuwa Makarantu da Asibitin Kuɗi

Gudumar Majalisa Za Ta Hau Manyan Gwamnati, Za a Hana Su zuwa Makarantu da Asibitin Kuɗi

  • Majalisar wakilai ta fara duba dokar hana ma’aikatan gwamnati da iyalansu zuwa makarantu da asibitocin kuɗi
  • Dan majalisa, Amobi Ogah ya ce ma’aikata na ci gaba da wulakanta makarantun da asibitocin gwamnati da ke Najeriya
  • Ya bayyana cewa 'yan 'kasar nan sun kashe Dala biliyan 29.29 don jinya a 'kasashen waje tsakanin 2015 zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaMajalisar Wakilan Najeriya ta fara duba 'kudurin da ke neman hana ma’aikatan gwamnati da iyalansu zuwa makarantu da asibitoci masu zaman kansu.

Wannan kuduri mai taken “Private Institutions and Health Care Service Providers (Prohibition) Bill, 2025” ya tsallake karatu na farko a zaman majalisar da aka yi ranar Talata.

Zaman majalisar wakilai ta kasa
Majalisa za ta waiwayi ma'aikatan gwamnati Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa ɗan majalisar wakilai daga jihar Abia, Amobi Ogah ya dauki nauyin ƙudurin da tuni ya wuce siraɗi na farko.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda Najeriya ke tafka asarar Naira tiriliyan 21.1 duk shekara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana son hana ma'aikatan gwamnati asibitin kuɗi

Business Day ta wallafa cewa Ogah ya ce ƙudurin zai hana dukkannin ma’aikatan gwamnati da iyalansu zuwa makarantu da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a Najeriya.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan zaman majalisar, Ogah ya bayyana cewa manufar kudurin shi ne dawo da sahihancin ayyuka a makarantu da asibitocin gwamnati.

Ya ce shugabannin baya irin su Ahmadu Bello, Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo da Tafawa Balewa duk sun halarci makarantun gwamnati.

Ogah ya ce:

“Yanzu kuwa sai kaga ma’aikatan gwamnati na yawan komawa cibiyoyin masu zaman kansu da na kasashen waje don ilimi da lafiya. Wannan ba wai kawai yana cutar da tattalin arzikin kasa ba ne, har ma yana rage martabar cibiyoyinmu na gwamnati."

Ɗan majalisa ya fusata

Ɗan majalisar ya bayyana takaici a kan yadda ƴan Najeriya ke kashe maƙudan kuɗi wajen neman lafiya da ilimi a ƙasashen wajen.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2

Yan majalisar wakilan Najeriya
Majalisa na son hana ma'aikata zuwa asibitin gwamnati Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

A kalamansa:

"A shekarar 2024, Najeriya ta ware N1.336trn ne kawai don harkar lafiya, amma 'yan Najeriya na kashe sama da $1bn duk shekara wajen jinya a kasashen waje.”

Ogah ya bayyana cewa daga shekarar 2015 zuwa 2023 'yan Najeriya sun kashe dala biliyan 29.29 wajen neman lafiya a kasashen waje.

Sannan a cikin watanni ukun farko na 2024, an kashe Dala miliyan 38.17 wajen karatu a kasashen waje.

Ya ce lokaci ya yi da za a dawo da kwarin gwiwa a kan cibiyoyin gwamnati domin gina martabar Najeriya a idon duniya.

An hana Sanata Natasha shiga majalisa

A wani labarin, mun wallafa cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Sanata Natasha ta iso majalisar cikin wata mota kirar SUV mai launin baƙi tare da rakiyar magoya bayanta, sai dai ta gamu da cikas yayin da jami'ai suka hana ta shiga.

Majalisar Dattawa ta gargadi Sanata Natasha da kada ta ƙara yunkurin komawa kujerarta ta hanyar amfani da karfi da yaji, tana mai cewa kotu ba ta ce a maida ta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng