"An Kusa Fara Ganin Saƙon Kudi," Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Biyan Ƴan N Power Kuɗinsu

"An Kusa Fara Ganin Saƙon Kudi," Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Biyan Ƴan N Power Kuɗinsu

  • Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana shirinta na biyan haƙƙokin ƴan N-Power da aka riƙe masu tun 2022
  • Mataimakin shugaban Majajalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da hakan bayan wani taron sasanci da ya jagoranta a Abuja
  • Ministan harkokin jin kai ya ce sun tarar da an sa kuɗin da za a biya ƴan N-Power a kasafin 2022 da na 2023 amma kuma ba a fitar da kuɗin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi alƙawarin biya bashin Naira biliyan 81 na kuɗaɗen masu cin gajiyar shirin N-Power da aka riƙe.

Majalisar Dattawa ce ta bayyana hakan yau Talata, 22 ga watan Yuli, 2025 a Abuja bayan wani taron sasanta tsakanin Gwamnatin Tarayya da matasan N-Power.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2

Shugaba Tinubu da ƴan N-Power.
Majalisar Dattawa ta sasanta gwamnatin tarayya da ƴan N-Power Hoto: N Power
Source: UGC

Punch ta tattaro cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ne ya jagoranci taron domin sasanta tsakanin Gwamnatin Tarayya da wakilan matasan N-Power da lauya Abba Hikima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta sasanta da ƴan N-Power

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Barau ya ce tattaunawar ta yi armashi, kuma an cimma matsaya cewa nan ba da jimawa ba ƴan N-Power za su fara ganin saƙon haƙƙoƙinsu.

"Masu cin gajiyar shirin N-Power sun zo nan sun kawo mana kukansu, suka nemi mu shiga tsakani, na kira minista kuma ya amsa. Mun zauna an tattauna kuma an fahimci juna.
"An tabbatar wa matasan N-Power cewa gwamnati na shirin biyansu kuɗinsu. Da suka ga da gaske gwamnatin take za ta biya, sun amince su janye matakin shari'a da suka fara ɗauka."
“Wannan gwamnati ce ta kowa, a shirye take ta amsa koken mai koke karkashin shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Tinubu, ba za a tauye wa kowa hakkinsa ba."

Kara karanta wannan

Duk da suna cikin hadaka, El Rufai da Peter Obi sun ki komawa ADC, an ji dalili

- Sanata Barau Jibrin.

Me ya hana biyan kuɗin N-Power a baya?

Ministan Harkokin Jin Kai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa bashin ya samo asali ne daga kasafin kudin 2022 da na 2023 wanda aka sa kudin ƴan N-Power amma ba a fitar da kudin ba.

“Mun yarda cewa an riƙe masu kudi. Wannan bashin na cikin kasafin kudin 2022 da 2023, amma ba a sanya su a kasafin 2024 da 2025. Za mu biya su kuɗinsu kafin ƙarshen 2025," in ji shi.
Ministan harkikin jin kai ya kwantar da hankulan ƴan N-Power.
Matsalar da aka samu har kuɗin N-Power suka maƙale Hoto: Yilwatda
Source: Twitter

N-Power: An janye ƙarar da aka shigar a kotu

Lauya Abba Hikima, wanda ya wakilci matasan N-Power, ya tabbatar da cewa sun dakatar da shari’ar saboda tabbacin da aka ba su a taron da Majalisar Dattawa ta shiga tsakani.

A sakon da ya wallafa a Facebook, Abba Hikima ya ce:

"Minista ya tabbatar mana cewa da zarar an fara aiwatar da kasafin kudin 2025, za a fara biyan haƙƙoƙin ƴan N-Power. Muna godiya ga Mataimakin Shugaban Majalisar da sauran jami’an gwamnati da suka shiga tsakani."

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya," ADC ta tona abin da gwamnatin Tinubu ta yi a rasuwar Buhari

Matasan N-Power sun maka Tinubu a kotu

A baya, kun ji cewa matasan da suka amfana da shirin N-Power sun maka gwamnatin Bola Tinubu APC a kotu kan kuɗaɗensu da suka biyo bashi.

Masu ƙarar sun nemi kotu ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya su diyyar N5bn sannan kuma ta biya su kudaden da suke bi.

Shirin N-Power wani tsari ne da tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari ya kafa a watan Yunin 2016 don rage zaman banza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262