Sanata Natasha Ta Nuna Yatsa ga Majalisa bayan an Hana Ta Shiga
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta fusata bayan da jami'an tsaro suka hana ta komawa bakin aiki a majalisar dattawa
- Ta nuna takaicinta kan yadda aka hana ta komawa kujerarta duk da cewa ta sanar da majalisar ranar da za ta dawo
- Sanata Natasha ta yi zargin cewa majalisar ta koma wurin karya doka ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya, ta yi magana kan hana ta shiga zauren majalisar dattawa.
Sanata Natasha ya bayyana cewa ƴan majalisar sun zama masu karya doka a ƙarƙarshin Godswill Akpabio.

Source: Facebook
Sanata Natasha ta yi magana ne lokacin da take zantawa da manema labarai s harabar majalisar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Natasha ta gamu da cikas a majalisa
A ranar Talata dai, jami'an tsaro sun hana Sanata Natasha shiga cikin majalisar dattawa domin komawa bakin aiki.
Sanatar wadda aka dakatar na tsawon watanni shida kuma kotun tarayya ta ba da shawarar a maida ta, ta zargi shugabannin majalisar da bijirewa kotu, tana mai cewa "majalisar dattawa ta koma mai karya doka."
Yunkurin Sanata Akpoti-Uduaghan na komawa bakin aikinta a majalisar ya biyo bayan hukuncin da kotun tarayya ta yanke a ranar 4 ga Yuli, 2025, inda aka bayyana dakatarwar da aka yi mata a matsayin wanda ya yi tsauri.
Kotun ta umarci a dawo da ita bakin aiki, kuma Sanatar ta riga ta aika da takardun hukuncin zuwa ga majalisar dattawa, inda ta bayyana niyyarta ta komawa aiki a ranar Talata, 22 ga watan Yulin 2025.
Sanata Natasha na son komawa kujerarta
The Cable ta ce da take magana da manema labarai a ƙofar majalisar tarayya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta nuna ƙudurinta na dawowa kan kujerarta.
“Wannan magana ce a kaina da kuma wata sanata da aka zaɓa da ke shirin shiga zauren majalisa domin ci gaba da ayyukanta, kamar yadda jama’ar Kogi ta Tsakiya suka ba ni amanar su."
“Abin takaici ne cewa yau, 22 ga Yuli, 2025, duk da cewa na sanar da majalisar ta wasiƙu biyu cewa zan dawo bakin aiki a yau, amma an hana ni."
“Abu na farko da ya ba ni mamaki shi ne yawan jami’an ƴan sanda masu makamai da muka tarar a waje, da suka tsaya cikin shiri da bindigogi, suna fuskantar wata sanata mace da ba ta da wani makami."
“Abu na biyu kuma shi ne yadda majalisar dattawa ƙarƙashin jagorancin Akpabio ta yanke shawarar zama masu karya doka, ta hanyar hana ni shiga domin na ci gaba da aikina."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Source: Facebook
Sanata Natasha ta ja kunnen Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi gargaɗi ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Ta buƙaci Sanata Akpabio da ya daina ɗaukar kansa kamar ya fi ƙarfin doka bayan an hana ta shiga majalisa.
Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta kuma nuna takaicinta kan yadda aka hana ta komawa bakin aiki duk da umarnin kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

