Bayan Mutuwar Buhari, Tsohon Gwamna Ya Ji Kunya kan Kalamansa gare Shi da Fulani
- Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom ya yi magana game da alakarsa da marigayi Muhammadu Buhari
- Ortom ya ce bai tsani Buhari ba kamar yadda ake zargi amma ya soki salon yaki da matsalar tsaro a jiharsa
- A cewar Ortom, dole ya fito ya yi magana don kare mutanensa daga hare-haren makiyaya, yana mai cewa ya yi aikinsa ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Tsohon Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, ya magantu game da sukar gwamnatin Muhammadu Buhari
Ortom ya karyata zargin cewa yana ƙin marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari saboda Fulani ne, sai ya bayyana ainihin niyyarsa kan haka.

Source: Facebook
Musabbabin sukar Buhari da Ortom ke yi
Ortom ya fadi haka yayin hira da Channels TV a ranar Litinin, inda ya kare kansa da cewa dole ne ya fito fili ya kare mutanensa.

Kara karanta wannan
Bayan Rasuwar Buhari, Sheikh Pantami ya yi magana kan takarar da ake so ya nema a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan na daga cikin gwamnoni a wancan lokaci da suke sukar gwamnatin tarayya wanda marigayi Buhari ke jagoranta.
Sannan ya ce ya soki gwamnatin tarayyar ne kawai saboda gazawa wajen shawo kan matsalar tsaro a jiharsa.
Ya ce kawai yana yin aikinsa ne a matsayin jagora a jiharsa duba da irin matsalolin da take fuskanta a wancan lokaci.
A cewarsa:
"Ban tsani Buhari ba, ban tsani gwamnatinsa ba, ban tsani ko wani ɗan Fulani ba, abin da nake tsayawa a kai shi ne, an zaɓe ni domin samar da tsaro da walwala ga mutanena.
"Ina yin aikina ne kawai, kuma na zargi gwamnatin da ta gabata saboda gazawarta wajen shawo kan matsalolin tsaro da muke fama da su.
"Ba zan iya kallo kawai ba ina ci gaba da birne mutane ba, dole na fadi gaskiya, amma ba nan na tsaya ba. Gwamnatina ta samar da mafita da muka yi imani da ita."

Kara karanta wannan
'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

Source: Instagram
Matsalar da Ortom ke suka a gwamnatin Buhari
Ortom ya ce da gwamnatin Muhammadu Buhari ta goyi bayansa da shirin da ya kawo, da matsalar tsaro a Benue ta zama tarihi a yau.
Ya ce ya fuskanci matsin lamba da bacin rai a zamanin Buhari, yana cewa shirin Ruga da sauran makamantansa karya ce kawai ba da gaske ake yi ba.
Tsohon gwamnan ya dage da cewa ba rikicin manoma da makiyaya ne ke faruwa a Najeriya ba, illa kawai wasu makiyaya ne ke kai farmaki kauyuka suna kashe mutane.
Ya kara da cewa suna lalata gonaki, suna yi wa mata fyaɗe da aikata wasu mugayen laifuffuka da suka haddasa asara ga al'umma.
Ortom ya magantu kan aiki da Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yi magana kan dalilinsa na yi wa PDP makarkashiya a zaɓen 2023
Ortom ya bayyana cewa ya ƙi goyon bayan PDP ne a zaɓen 2023 saboda ƙin ba ɗan yankin Kudu takarar shugaban ƙasa a shekarar.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa ya yi farin ciki sosai da ɗan Kudancin Najeriya ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng
