Sarkin Daura Ya Fadi Dalilin Goyon Bayan Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027
- Mai martaba, Sarkin Daura ya nuna goyon bayansa ga tazarcen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027
- Alhaji Umar Farouq-Umar ya bayyana cewa yana goyon bayan shugaban ƙasan ne saboda karamcin da ya yi wa masarautarsa da jihar Katsina
- Ya nuna jin daɗinsa kan yadda Shugaba Tinubu ya karrama marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Sarkin Daura da ke jihar Katsina, Alhaji Umar Farouq-Umar, ya bayyana dalilin goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Alhaji Umar Farouq-Umar ya ce yana goyon bayan Tinubu ne saboda girmama masarautar Daura da jihar Katsina ta hanyar yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari jana’izar da ta dace da matsayin sa.

Source: Facebook
Uwargidan Tinubu ta je ta'aziyyar Buhari
Jaridar Daily Trust ta ce Sarkin ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke Daura a ranar Asabar, lokacin da yake karɓar tawagar matan gwamnonin Najeriya ƙarƙashin jagorancin uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar ta je Daura ne domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Premium Times ta ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ne ya tarbi tawagar, inda ya jagorance su zuwa Daura domin gaisuwar ta’aziyya.
Sarkin, yayin da yake gode wa Shugaba Tinubu saboda jana’izar ƙasa da aka shirya wa Buhari, ya miƙe tsaye yana ta ambaton sunan Shugaba Tinubu, tare da nuna goyon bayan sake zaɓensa.
Meyasa Sarkin Daura ke goyon bayan Tinubu?
"Ina godiya ga Shugaba Bola Tinubu, mutum nagari wanda na shafe fiye da shekaru 30 ina tare da shi. Duniya na iya shaida abin da Shugaba Tinubu ya yi wa wannan jiha da masarautar Daura."
"Ina da shekara 97 a duniya, ban taɓa ganin irin girmamawar da wani shugaban ƙasa ya yi wa wani marigayi kamar yadda Tinubu ya yi wa Muhammadu Buhari ba."
“Shi da kansa ya zo, ya kwashe kwanaki yana makoki, ya ayyana hutu na ƙasa a matsayin girmamawa, ya amince da amfani da jirgin shugaban ƙasa domin ɗauko gawar, kuma ya kasance cikin gudanar da duk shirye-shirye daga farko har ƙarshe."
"Yanzu kuma ya turo da uwargidansa, da uwargidar mataimakin shugaban ƙasa da kuma matan gwamnoni."
"Ba za mu taɓa mantawa da wannan girmamawa da karramawa da shugaban ƙasa ya nuna mana ba, za mu saka masa. Wannan shi ne dalilin da ya sa a 2027 za mu zaɓi Tinubu."
- Alhaji Umar Farouq Umar

Source: Facebook
PDP ta ragargaji Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi kalamai masu kaushi kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Najeriya mai kishin ƙasa da zai kaɗa ƙuri'arsa ga Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.
Jam'iyyar adawar ta nuna cewa Shugaba Tinubu ya zama baƙar haja kuma wa'adi ɗaya kawai zai yi a kan karagar mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng

