"Dan Allah Ina Rokon Alfarma," Autar Marigayi Buhari Ta Saki Kalamai Masu Taɓa Zuciya
- Ƙaramar ɗiyar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta roki ƴan Najeriya alfarmar yi wa mahaifinta addu'o'in neman rahama
- Noor Buhari ta bayyana cewa zuciyarta na fama da raɗaɗi tsawon kwanaki bakwai da ta yi ba tare da mahaifinta
- Ta ce wasu kaburburan sun fi daular duniya haske, tana mai ƙara godiya ga dukkan waɗanda suka taya iyalanta jimamin rashin Buhari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Noor, ƙarama daga cikin ’ya’yan tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ta bayyana alhinin da kuma yadda rasuwar mahaifinta ta taɓa mata zuciya.
A cewarta, kabarin mahaifinta, Buhari ya fi daular duniya haske, tana mai cewa kwanaki bakwai da suka wuce sun kasance masu raɗaɗi da nauyin zuciya.

Source: Instagram
Noor Buhari ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Istagram bayan kwanaki bakwai da rasuwar tsohon shugaban ƙasar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Noor ta sake jimamin rasuwar Buhari
Autar marigayin ta bayyana cewa rayuwa ta ɗauki wani sabon salo mai cike da kunci da raɗaɗi tun bayan rasuwar mahaifinta.
“Wasu kaburbura sun fi daular duniya haske, saboda waɗanda ke ciki sun rayu ne domin Allah kaɗai,” in ji ta.
Ta haɗa wannan magana da wani tsohon faifan bidiyo nata tare da iyayenta. Ta bayyana irin girman ramin da mutuwar mahaifinta ta bari a zuciyarta.
“Yanzu mako guda ke nan da Baba ya koma ga Ubangijinsa. Kowanne yini tun daga lokacin ya kasance shiru, da nauyi, sannan komai ya sauya ba kamar da ba.
"Inna lilLahi wa inna ilayhi raji’un. Gaskiya daga Allah muka zo kuma gare Shi za mu koma," in ji Noor.
Noor ta ƙara yiwa mahaifinta addu'ar rahama
Noor, wacce ta kasance mai natsuwa da nisantar fitowa fili tsawon shekaru, ta haɗa da addu’a domin neman rahama, gafara da jinƙai ga mahaifinta, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa
“Ina roƙon Allah Ya yi masa rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya shi a cikin salihai. Allah ya sanya kabarinsa a lambun Aljanna, mai cike da haske,” in ji ta.

Source: Facebook
Autar Buhari ya nemi alfarma daga ƴan Najeriya
Ta kuma yi amfani da wannan dama don nuna godiya ga ’yan Najeriya da masoya bisa tallafi da tausayin da suka nuna a lokacin da iyalinsu ke cikin jimami.
“Muna godiya ga duk wanda ya kira, ya yi addu’a, ya aiko saƙo, ko ya turo mana da kalmomi na ta’aziyya. Addu’arku da alherinku sun fi abin da kalmomi za su iya bayyana.
“Don Allah ku ci gaba da saka Babana a cikin addu’arku. Allah ya haɗa mu da masoyanmu a cikin Aljanna wata rana. Ameen."
- Noor Buhari.
Mamman Daura ya fitar da saƙon godiya
A wani rahoton, kun ji cewa Mamman Daura ya miƙa sakon godiya da duka waɗanda suka taya iyalan Muhammadu Buhari makokin rashinsa.
A madadin iyalai da dangin marigayin, ya yi godiya ga ‘yan Najeriya da sauran mutane daga kasashe daban-daban da suka jajanta musu bayan rasuwar Buhari.
Malam Mamman Daura ya bayyana cewa dangin sun samu goyon baya daga shugaba Bola Ahmed Tinubu da uwargidansa, Sanata Remi Tinubu.
Asali: Legit.ng
