Yan Najeriya Sun Koka da Tsarin Ɗaukar Ma'aikatan Gwamnati, Sun Gano Matsaloli

Yan Najeriya Sun Koka da Tsarin Ɗaukar Ma'aikatan Gwamnati, Sun Gano Matsaloli

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an buɗe sabon shafin yanar gizo domin 'yan kasa su nemi guraben aiki a hukumomin gwamnati
  • Hukumomin da za a dauki ma'aikatan sun hada da Hukumar Tsaron Fararen Hula, Hukumar Gyaran Hali da Hukumar Kashe Gobara ta kasa
  • Daga cikin martanin jama’a, wasu sun bayyana shakku cewa tuni an riga an ɗauki mutane kafin buɗe shafin da ke fuskantar matsala a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wasu daga cikin mazauna 'kasar nan sun bayyana shakku a kan tsarin ɗaukar sababbin ma'aikatan gwamnatin tarayya.

A baya, gwamnatin ta ayyana shirin fara ɗaukar ma'aikata, sai dai an samu tsaiko sakamakon wata 'yar matsala.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Gwamnati ta sake bude shafin daukar ma'aikata Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Amma a sakon da shafin yaɗa labaran shugaban kasa, Bola Tinubu ya wallafa a shafin X, an ce komai ya dawo daidai kuma jama'a za su ci gaba da kokarin aika bayanansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina Dikko Radda ya yi bayani daga asibiti bayan haɗarin mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta fara shirin ɗaukar ma'aikata

A cikin sakon, an wallafa cewa yanzu haka an buɗe shafin yanar gizo don ba 'yan kasa damar neman guraben aikin da ake da su a wasu hukumomi.

Hukumomin da ake buƙatar ɗaukar ma'aikatan sun haɗa da Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Hukumar Kashe Gobara da ta Tsaron Fararen Hula.

Sakon ya ce:

"Za a sake buɗe shafin yin rajista don neman aiki a Hukumar shige da fice ta kasa, Hukumar Tsaron Fararen Hula, Hukumar Gyaran Hali, da Hukumar Kashe Gobara daga ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025."

Jama'a sun fara neman guraben aikin gwamnati

Tuni wasu daga cikin 'yan kasar nan suka fara ƙoƙarin shiga shafin domin su yi rajista ko za su dace.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Jama'a sun fara neman gurbin aikin gwamnati Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Amma an samu waɗanda ke ganin wannan magana ce kawai, domin an riga an ɗauki waɗanda ake so su cike guraben.

@ClementEmosivwe ya ce:

"An riga an yi wa shafaffu da mai rajista a lokacin da yaran talakawa ba sa iya shiga shafin. Yanzu shafin ba ya aiki yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

An zo wajen: EFCC ta fara bincikar gwamnoni masu ci a Najeriya

@AdetunjiAdewolu ya wallafa cewa:

"Allah Ya ba da sa’a. Da fatan cancanta za a duba, ba wanda ka sani ba."

Baya ga fatan da wasu ke yi na cewa gwamnati za ta yi adalci a wajen ɗaukar ma’aikatan, an samu wadanda suka ce suna ƙoƙarin shigar da bayanansu, amma shafin ya ƙi aikin da ya dace.

@Marcus Daushe ya ce:

"Ba a samun damar shigar da bayanai, na gwada yanzu. Sashen da ke kula da bangaren su duba."

@A2victor_devOp ya ce:

"Me zai hana ku ɗauko ƙwararru da suka san harkar don daidaita shafin? Nawa gwamnati za ta kashe ne ma?"

Gwamnati ta bude shafin daukar ma'aikata

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Tarayya ta buɗe sabon shafin yanar gizo domin ɗaukar sababbin ma’aikata a wasu manyan hukumomin tsaro da agaji a ƙasar nan.

Wannan na zuwa ne a matsayin wani mataki na rage rashinsa aikin yi a tsakanin matasa da kuma cike gibin ma’aikata, wanda ake sa ran zai bunkasa ayyukan hukumomin.

Hukumomin da za a ɗauki ma’aikata a cikinsu sun hada da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC), Hukumar Kashe Gobara da Hukumar Gidajen Gyaran Hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng