An Samu Karaya yayin da Gwamna Radda da Jami'ansa Suka Yi Hadari
- Gwamna Dikko Radda ya tsira daga hatsarin mota a hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi da yamma
- Gwamnatin Katsina ta ce gwamnan na cikin koshin lafiya bayan duba lafiyarsa a manyan asibitoci
- Rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin jami'an gwamnatin jihar da ya ke tafiya tare da Dikko Radda ya karye
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa gwamnan jihar, Dikko Umar Radda, bai samu mummunan rauni ba bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi.
Gwamna Dikko Radda ya yi hadari ne a hanya daga Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuli, 2025.

Source: Facebook
BBC Hausa ta rahoto cewa gwamna Dikko Radda ya yi hadarin ne tare da wasu jami'an gwamnatin shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatsarin ya faru ne bayan wata mota kirar Golf ta yi karo da motar da gwamnan ke ciki yayin da yake kan hanyar Daura domin cigaba da jimamin rasuwar shugaba Muhammadu Buhari.
Rahotanni daga hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa gwamnan ya samu kulawar gaggawa a asibitin Daura kafin a dawo da shi zuwa babban asibitin koyarwa na Katsina.
Hadari: Halin da gwamna Radda ke ciki
Hadimin gwamnan Katsina, Maiwada Dammallam, ya tabbatar da cewa bayan isar da gwamnan zuwa asibitin Daura, an ba shi taimakon farko kafin a garzaya da shi zuwa Katsina.
“Ina tabbatar muku da cewa daga binciken da ƙwararrun likitoci suka yi, babu wata matsala mai girma a lafiyar gwamna Radda. Yanzu haka yana cikin koshin lafiya,”
In ji Dammallam
An samu karaya a tawagar gwamna Radda
A cewar Dammallam, akwai wasu mutane uku da ke cikin motar tare da gwamnan a lokacin da hatsarin ya faru.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, Hakimin Kuraye da kuma Alhaji Shamsu Funtua na cikin wadanda suke tare da gwamnan.
Duk da cewa wani rahoto ya nuna cewa ba su samu babban rauni ba, Aminiya ta wallafa cewa mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya ce an samu karaya:
"Gaskiya ita ce, Gwamna Dikko Umar Radda bai samu mummunar rauni ba. Duk da cewa wani ɗan majalisar tarayya da ke tare da shi ya samu karaya da kuma Shugaban Ma’aikata ya samu dan rauni, amma gwamnan bai ji ciwo mai tsanani ba."

Source: Facebook
Motocin da Dikko Radda ke tafiya da su
Maiwada Dammallam ya ce tun bayan rasuwar shugaba Muhammadu Buhari, gwamna Radda ya dauki matakin rage yawan motocin da ke raka shi zuwa Daura domin rage kashe kudi.
“Kamar mota uku ne kawai a cikin tawagar gwamnan saboda yana yawan kai ziyara Daura tun rasuwar Buhari. Wannan tsari ne na sassauta tafiye-tafiye,”
Dikko Radda ya yi bayani a asibiti
A wani rahoto, kun ji cewa gwamna Dikko Umaru Radda ya fito ya yi magana bayan hadarin motar da ya yi.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi hadari ne yayin da ya ke tafiya daga Katsina zuwa Daura, gidan Muhammadu Buhari.
Legit ta rahoto cewa gwamna Dikko Radda ya mika godiya da mutanen da suka taya shi da addu'a bayan jin labarin hadarin.
Asali: Legit.ng


