"Ka Makara": ADC Ta Tono Shirin Shugaba Tinubu kan Arewa
- Jam'iyyar ADC ta ƴan haɗaka ta caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan naɗe-naɗen muƙaman da ya yi a kwanan nan
- ADC ta bayyana cewa naɗe-naɗen muƙaman ba komai ba ne face ƙoƙarin samun yardar ƴan Arewa waɗanda aka yi watsi da su
- Ta bayyana cewa yanzu fa kan mage ya waye domin muƙaman ba za su ƴan Arewa su manta da yadda aka yi watsi da su ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi martani kan sababbin naɗe-naɗen muƙamai da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Jam'iyyar ADC ta bayyana sanarwar sababbin naɗe-naɗen muƙaman na Shugaba Tinubu a matsayin ƙoƙarin samun yardar ƴan Arewa.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi ya fitar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC ta soki Tinubu kan ba da muƙamai
ADC ta bayyana cewa muƙaman sun zo a a makare bayan da yankin Arewa ya dawo daga rakiyar Tinubu sakamakon watsi da shi da ya yi.
A cikin sanarwar ADC ta ce ba zai yiwu Tinubu ya yi watsi da wani yanki na ƙasa na fiye da watanni 25 ba, sannan ya yi tsammanin yabo saboda ya tuna a wata na 26 cewa Najeriya ta fi jihar Legas girma ba.
A cewar ADC, waɗannan muƙaman ba komai ba ne face ƙokarin kare kai na siyasa kuma yunkuri ne na gaggawa don rufe raunin da aka haifar wa Arewacin ƙasar nan ta hanyar watsi da su.
ADC ta ce ba za a yaudari ƴan Arewa ba
“Fiye da shekara guda wannan gwamnati ta rufe ido yayin da ƴan bindiga ke addabar ƙauyuka a Arewa, manoma suka bar gonakinsu, kuma tattalin arzikin karkara ya durƙushe sakamakon cire tallafin man fetur ba tare da shiri ba."

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: Tsohon gwamnan PDP ya fadi dalilin yin aiki don kayar da Atiku a 2023
"Yanzu kuma, bayan jin zafin fushin jama'a da kuma bayyanar haɗakar ƴan adawa da ke ƙara karɓuwa a Arewa da fadin ƙasa baki ɗaya, Shugaba Tinubu kwatsam ya fara tuna cewa akwai ƴan Najeriya da ke buƙatar a ba su muƙamai a wajen Legas."
“Kusan dukkan manyan manufofin wannan gwamnati, daga cire tallafin man fetur zuwa mafi yawan naɗe-naɗen siyasa, an yi su ba tare da Arewacin ƙasar nan yana kan teburin yanke shawara ba."
"Yanzu da sakamakon waɗancan matakai ya fara bayyana a fili, shugaban ƙasa yana ta bayar da muƙamai a matsayin lada ko diyyar kwantar da hankali."
“Amma ƴan Arewa, a matsayinsu na masu faɗa a ji a ƙasarmu da sauran yankuna, sun yi wayon da ba za a yaudaresu da waɗannan ƙananan muƙaman ba."
"Mutanen Arewa sun fahimci abin da Shugaba Tinubu ke yi, kuma sun gano cewa ba da gaske bane."
- Mallam Bolaji Abdullahi

Source: Twitter
ADC ta soki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan jana'izar Muhammadu Buhari.
Jam'iyyar ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da sanya siyasa a cikin jana'izar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya.
Ta bayyana cewa taron majalisar zartaswa da aka shirya domin karrama Buhari, ba komai ba ne face wasan kwaikwayon yara.
Asali: Legit.ng
