Pantami Ya Sanar da Mutuwar Jigon PDP, Ya Shawarci Al'umma game da Jana'izarsa

Pantami Ya Sanar da Mutuwar Jigon PDP, Ya Shawarci Al'umma game da Jana'izarsa

  • Jam’iyyar PDP a Gombe ta yi babban rashi bayan rasuwar tsohon sakataren yankin Arewa maso Gabas, Kabiru Bappah Jauro
  • Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin rasuwar Bappah Jauro inda ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin
  • Marigayin ya rasu a wani asibiti na Turkiyya da ke Abuja bayan fama da doguwar rashin lafiya, PDP ta ce rasuwar ta yi matuƙar taba ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta yi rashin jigonta wanda ya rike mukamai da dama a matakin kasa baki daya.

Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar Kabiru Bappah Jauro inda ya mika sakon ta'aziyyarsa.

Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar jigon PDP
Pantami ya sanar da rasuwar jigon PDP a Gombe. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Pantami ya yi ta'ziyyar rasuwar jigon PDP

Farfesa Isa Ali ya tabbatar da haka ne a shafinsa na Facebook a cikin daren yau Lahadi 20 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya nuna kaduwarsa bayan rashin da aka yi inda ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Ya kuma shawarci dukan wadanda suka samu dama da su halarci jana'izar marigayin da za a yi yau Lahadi a Gombe.

A cikin rubutunsa ya ce:

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!
"Muna mika ta'aziyyar rasuwar Alhaji Kabiru Bappah Jauro zuwa ga iyalansa da dukkan yan'uwa, musamman Hajiya Muniraat.
"Za a yi masa Sallar Janazaa a Masallacin 'Federal Teaching Hospital' Gombe, gobe Lahadi da karfe 4:00 in sha Allah, ya na da muhimmancin ga wanda ya samu dama ya halarci sallar."

A karshe, Pantami ya roki Allah ya sa Aljannah ce makomarsa tare da iyaye da malamai da zuri'a baki daya.

PDP ta sanar da rasuwar jigonta a Gombe
Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a Gombe. Hoto: Legit.
Source: Original

PDP ta yi jimamin rasuwar jigonta a Gombe

Reshen jam’iyyar PDP na jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan shugabanninta, Kabiru Bappah Jauro.

Kara karanta wannan

'Yadda Buhari ya yaƙi Bankin Duniya da IMF domin kare talakan Najeriya'

Marigayin ya rasu ne da yammacin Asabar a wani Asibitin Turkiyya da ke Abuja, bayan fama da doguwar rashin lafiya, ya bar duniya yana da shekaru 60.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, A.A. Dukku, ya sanya wa hannu, PDP ta bayyana rasuwar a matsayin mai matuƙar ɓacin rai, amma ta miƙa wuya ga ƙaddarar Allah.

Kabiru Bappah Jauro ya kasance tsohon sakataren yankin Arewa maso Gabas na PDP, kuma ana kallonsa a matsayin ɗan jam’iyya na gaskiya da ya taka rawa sosai.

Kafin rasuwarsa, Kabiru ya kasance jagora mai tsayawa kan gaskiya, wanda basirarsa da ƙwarewar siyasa suka taimaka wajen tafiyar da al’amuran PDP a Arewa maso Gabas.

Yan bindiga sun harbi dan takarar gwamnan PDP

Kun ji cewa ‘yan bindiga sun harbe dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Abuja yayin da aka garzaya da shi asibiti domin tiyata.

Yan bindiga sun kai harin ne kan jigon PDP, Jude Ezenwafor, a kusa da Wuse 2, Abuja ranar Juma’a da dare.

Ezenwafor shi ne PDP ta zaba domin yi mata takara a zaben gwamna da za a gudanar a watan Nuwambar 2025 a jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.