Kallo Zai Koma Majalisa yayin da Sanata Natasha Ta Sha Sabon Alwashi

Kallo Zai Koma Majalisa yayin da Sanata Natasha Ta Sha Sabon Alwashi

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta taɓo batun komawa kujerarta a majalisar dattawa
  • Natasha ta bayyana cewa za ta koma majalisar dattawa a mako mai zuwa kuma ta riga ta sanar da mahukunta
  • Ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata daga majalisa bai hana ta gudanar da ayyuka ba ga mutanen mazaɓarta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana lokacin da za ta koma majalisar dattawa.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jaddada cewa za ta koma kujerarta a majalisar dattawa a ranar Talata, 22 ga watan Yuli, 2025, bisa hukuncin kotu.

Sanata Natasha ta sha alwashin komawa majalisa
Sanata Natasha ta ce za ta koma kujerarta a majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate, Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa Sanata Natasha ta bayyana hakan ne a wajen wani shirin ba da horo a mazaɓarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha dai za ta koma majalisar ne duk da cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ɗaukaka ƙara a shari'ar da suke yi.

Kara karanta wannan

Akpabio ya isa Daura don ta'aziyyar Buhari, ya fadi dabi'un tsohon shugaban

Wata babbar kotun tarayya dai ta soke dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha har na tsawon watanni shida.

Sanata Akpoti-Uduaghan, wadda ke cikin mazabar da take wakilta domin gudanar da wani shirin horo na ƙarfafa gwiwar al’umma, ta ce dakatarwar da aka yi mata ba ta hana ta ci gaba da aiki a mazabarta ba.

Sai dai ta ce dakatarwar ta hana ta sauke wani babban ɓangare na nauyin da ke kanta, wanda ya haɗa da daukar nauyin ƙudurori da ba da ra'ayinta kan batutuwan da ake tattunawa a zauren majalisar.

Yaushe Natasha za ta koma majalisa?

Ƴar majalisar ta bayyana cewa ta riga ta aika da wasiƙa zuwa Majalisar Dattawa domin sanar da su niyyarta ta komawa aiki a ranar Talata mai zuwa.

"Ina da kusan wata biyu kacal kafin wa’adin watanni shida ya cika. Duk da haka, na sake rubuta wa Majalisar dattawa, na shaida musu cewa zan koma aiki a ranar 22 ga wata, wato Talata, da ikon Allah."
"Zan kasance a wurin, domin kotu ta yanke hukunci a kai. Yanzu suna ce-ce-ku-ce cewa umarni ne ba umarni ba ne, hukunci ne."

Kara karanta wannan

Jagoran yan ta'adda ya shiga hannu, ya fara ambato abokan hulɗarsa bayan ya ji matsa

"Na taɓa bayyana cewa kowanne sanata yana da manyan ayyuka guda uku. Na farko shi ne harkokin dokoki, wato samar da dokoki da kuma duba yarjejeniyoyi."
"Na biyu shi ne sa ido wato kula da ministoci da hukumomin gwamnati. Na uku kuma wakilci ne wanda nake yi."
"Wannan yana nufin ina gano matsaloli da ƙalubalen da ke fuskantar al’ummata, sannan ina tabbatar da cewa na gabatar da su domin a saka su cikin kasafin kuɗin tarayya. Kuma na yi kyakkyawan aiki a wannan fanni. Hakika, ina kewar gabatar da kudirori a majalisa, amma hakan bai hana ni ci gaba da aiki ba."

- Sanata Natasha Akpoti -Uduaghan

Sanata Natasha za ta koma majalisa
Sanata Natasha ta sha.alwashin komawa majalisa Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Dalilin majalisa na ƙin dawo da Natasha

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta bayyana dalilin ƙin dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa suna jiran samun kwafin hukuncin kotu ne kafin su ɗauki mataki na gaba.

Sanata Yemi Adaramodu ya bayyana cewa sai lokacin da suka samu kwafin hukuncin suka yi nazari a kansa, sannan za su san abin da za su yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng