An Zo Wajen: EFCC Ta Fara Bincikar Gwamnoni Masu Ci a Najeriya

An Zo Wajen: EFCC Ta Fara Bincikar Gwamnoni Masu Ci a Najeriya

  • Wasu gwamnoni masu ci a hali yanzu za su fuskanci matsala bayan sun sauka daga kan mulki
  • Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai gwamnonin da suka fara bincike a kansu
  • Ya bayyana cewa da zarar sun sauka daga kan madafun iko, hukumar za ta ɗauki mataki na gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa yana bincikar wasu gwamnoni da ke kan mulki.

Shugaban na hukumar EFCC ya bayyana cewa hukumar tana gudanar da bincike kan gwamnoni 18 da ke kan mulki a halin yanzu.

EFCC na bincikar wasu gwamnoni
EFCC ta fara yin bincike kan wasu gwamnoni Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Ola Olukoyede ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a yayin wani shirin wayar da kai da aka gudanar a Legas a ranar Juma’a, 18 ga watan Yulin 2025, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Daga zuwa taimakon ƴan uwansu musulmi, matasa 4 sun rasu a Kano

Hukumar EFCC na bincikar gwamnoni

Shugaban na EFCC ya ce hukumar zata ɗauki mataki na gaba bayan wa’adin mulkin waɗannan gwamnoni ya kare.

An shirya wannan taro ne domin wayar da kai ga masu ruwa da tsaki, ciki har da masu shirya fina-finai da kuma masu canjin kuɗaɗe dangane da illolin da ke tattare da lalatawa da cin zarafin kuɗin Naira.

A lokacin zaman tambayoyi da amsoshi, shugaban EFCC ya bada misali da yadda aka kama wani tsohon gwamna a ƙasar Ingila saboda wani manajan otal ya ɗauka yana da tabin hankali, ganin yadda yake watsar da takardun kuɗin Biritaniya (pounds).

Olukoyede ya bayyana cewa wannan tsohon gwamna ya tsere daga Najeriya zuwa Ingila washegarin da ya miƙa mulki, rahoton TheCable ya tabbatar.

Yadda tsohon gwamna ya tserewa EFCC

"Zan ba ku misali da abin da muka fuskanta a EFCC. Akwai wani lokaci a ƙasar nan da muke bincikar wani gwamna. Ba sai sun gama mulki ba ne muke fara bincike."

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

“A halin yanzu da nake magana da ku, muna bincikar gwamnoni kusan 18 da ke kan mulki. Idan suka sauka daga mulki, sai mu ɗauki mataki na gaba."
“Wannan gwamnan an riga an fara bincikarsa tun yana kan mulki. Yana kammala wa’adin mulkinsa, washegari ya tsere zuwa Ingila domin kauce wa kamun EFCC."
"Makon da ya isa Ingila ya zo daidai da ranar zagayowar ranar haihuwarsa. Sai ya shirya bikin ranar haihuwarsa a otal ɗin da yake sauka."
“A yayin bikin, sai ya fara watsa takardun kuɗi fam 50 da fam 10. Sai aka kira manajan otal ɗin. Da ya sauko ya gan shi yana watsar da kuɗin, abin ya ba shi mamaki, domin bai taba ganin haka a rayuwarsa ba. Nan take sai ya kira 911."
“Da ƴan sanda suka iso, sai ya roƙe su da su kama tsohon gwamnan. An kama shi kuma aka shirya da za a saka shi cikin motar asibiti."
“Mutanen da suka raka shi, abokansa, ƴan uwa, da wasu gwamnoni biyu da suka je Ingila don bikin tare da shi sai suka sa baki. Suka ce bai haukace ba, domin manajan otal din ya dauka wannan tsohon gwamna mahaukaci ne."

Kara karanta wannan

An kutsa gidan Buhari, an samo yadda ya yi wata irin rayuwa da iyalansa

- Gwamna Ola Olakuyode

EFCC ta fara bincikar wasu gwamnoni
EFCC na bincike kan wasu gwamnoni masu ci Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

EFCC ta cafƙe tsohon shugaban majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta cafke tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Plateau, Moses Thomas Sule.

Hukumar EFCC ta cafke Moses Sule ne tare da wasu ƴan majalisar dokokin su 14 kam badaƙalar motoci.

An dai cafƙe su ne bayan sun ƙi dawo da motocin da gwamnatin jihar ta siya musu ƙafin a raba su da kujerunsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng