'Yan Bindiga Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka
- Ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki kan jami'an tsaro a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma a Najeriya
- Miyagun ƴan bindigan sun kai harin na kwanton ɓauna kan jami'an rundunar Askarawan Zamfara a ƙaramar hukumar Talata Mafara
- A yayin harin dai, an hallaka wasu daga cikin jami'an tsaron tare da ƙwace makaman da suke amfani da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai mummunan hari a garin Jangebe da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kashe mambobi biyar na rundunar Askarawan Zamfara (CPG) da kuma fararen hula mutum biyu.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara
Bisa bayanan da majiyoyi na tsaro suka bayyana, harin ya faru ne da rana, a ranar Juma’a, 18 ga watan Yulin 2025.
Lamarin ya auku ne lokacin da wasu jami’an CPG guda biyar, ciki har da kwamandan sashen su, suka je wata gona a bayan gari domin taimakawa wajen yin noma.
Sai dai yayin da suke cikin aikin gona, sai ƴan bindigan suka yi musu kwanton-ɓauna inda suka buɗe musu wuta suka kashe jami'an tsaron guda biyar nan take.
Baya ga hakan, wasu fararen hula guda biyu, namiji da mace da ke aiki a wata gona kusa da wurin, suma an harbe su har lahira a harin.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ƴan bindigan sun ƙwace bindigogi guda biyu ƙirar pump-action daga hannun jami’an tsaron da suka kashe.
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun fara wani gagarumin samame domin kamo masu laifin, tare da alwashin cewa ba za su bari su tsira ba, kuma za su gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.
Zamfara na fama da ƴan ƴan bindiga
Wannan hari na Jangebe ya ƙara tayar da hankali a jihar Zamfara, inda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara.

Source: Facebook
Harin ya sake jaddada buƙatar ƙarin tsaro a yankunan karkara da kuma ɗaukar tsauraran matakai don kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Mazauna yankin na cikin fargaba, suna rokon gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare su daga irin waɗannan munanan hare-hare da suka zama ruwan dare.
Ƴan sanda sun cafke riƙaƙƙen ɗan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, sun samu nasarar cafke wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da aka daɗe ana nema ruwa a jallo.
Ƴan sandan sun cafke Mati Bagio wanda aka kwashe shekara 11 ana neman sakamakon ayyukan ta'addancin da yake yi a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara.
An samu nasarar cafke Mati Bagio ne a gidansa da ƙaramar hukumar Giwa inda aka ƙwato makamai tare da wasu ababen hawa da ake zargin na sata ne.
Asali: Legit.ng

