Gwamna, Iyalan Sarki Sun Shiga Matsala bayan Birne Basarake bisa Tsarin Musulunci

Gwamna, Iyalan Sarki Sun Shiga Matsala bayan Birne Basarake bisa Tsarin Musulunci

  • Kungiyar mabiya addinin gargajiya ta ce zata maka gwamnatin Ogun da dangin marigayi Oba Sikiru Adetona a kotu
  • Kungiyar ICIR ta ce za ta dauki wannan mataki ne saboda watsi da dokokin al'adu wajen binne Sarki bayan ya rasu
  • Shugaban ICIR ya ce bin addinin Musulunci wajen birne Oba ya saba da Sashe na 55, sakin layi na biyu na dokar sarauta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Kungiyar Addinin Ifa (ICIR) ta ce za ta gurfanar da gwamnatin jihar Ogun da dangin marigayi Awujale na Ijebu.

Kungiyar ta ce za ta dauki matakin ne bayan birne marigayi Oba Sikiru Adetona, a kotu bisa zargin karya doka.

Za a gwamna a kotu kan binne Sarki
Mabiya addinin gargajiya za su maka Gwamna, iyalan Sarki a kotu. Hoto: Oba Sikiru Adetona.
Source: UGC

Mutuwar Sarki: Mabiya addinin gargajiya sun fusata

Punch ta ce kungiyar ta tabbatar da cewa an yi watsi da tsarin gargajiya wajen binne sarakuna da dama a jihar.

Kara karanta wannan

NELFund: Gwamnatin Tinubu za ta bude dandalin taimakawa dalibai samun aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ICIR ta sha alwashin gyara abin da ta kira sabawa da al'ada da kuma watsi da tsarin gargajiyar Yarbawa wajen baiwa sarki girmamawar karshe da hakkokin binne shi.

Sarkin Ijebu, wanda ya rasu ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 yana da shekaru 91, an tabbatar da binne shi ne bisa tsarin addinin Musulunci

Shugaban ICIR, Dakta Fayemi Fatunde Fakayode, ya tuna da hukuncin kotu da aka zartar lokacin da marigayi Awujale ke raye.

Ya ce hakan ya tabbatar da cewa dole ne a binne sarakuna bisa tsarin gargajiya na Yarbawa, ba bisa tsarin addinai kamar Musulunci ko Kiristanci ba, The Nation ta ruwaito.

Ya ce:

“Dangane da ce-ce-ku-cen da ke tattare da birne Oba Awujale na Ijebu-Ode a jihar Ogun, muna yabawa kungiyar Osugbo ta Ijebu-Ode bisa hakurinsu da jarumtar da suka nuna.
“Dangane da birne marigayi Oba Sikiru Kayode Adetona, ya kamata a tuna cewa an riga an yanke hukunci a lokacin da marigayi ke raye, tare da sabon kudirin doka a jihar."

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau na 18 da manyan sarakuna 8 da suka fi daɗewa a kan sarauta a Najeriya

An taso gwamna a gaba bayan binne marigayi Sarki
Za a maka gwamna, Iyalan Sarki a kotu bayan binne basarake. Hoto: Prince Dapo Abiodun.
Source: Facebook

Jana'iza: Gargadin yan addinin gargajiya ga limamai

An gargadi malaman Musulunci da limamai da suka birne basaraken cewa sun karya doka mai girma a masarautar.

Sanarwar ta ce:

Wannan mataki na daga cikin wata babbar makirci da nufin lalata al’adunmu da kuma shirin kawar da kabilar mu.”
“Limaman Musulunci da suka jagoranci binne Sarkin tare da Babban Limamin Ijebu-Ode sun karya doka kuma sun nuna rashin bin doka, abin da ya bayyana dabi’ar addininsu.
“Tsarin gargajiya tsarin da doka ke jagoranta ne, sabanin addinin Musulunci. Mabiya gargajiya za su dauki matakin doka da ya dace don neman hakki.”

An yi rigima a birne marigayi Sarki Musulmi

Mun ba ku labarin cewa sojoji sun hana yan addinin gargajiya shiga jana'izar fitaccen basarake da aka gudanar a bisa tsarin Musulunci.

An binne marigayi Oba Sikiru Adetona, bisa koyarwar Musulunci, inda aka yi masa addu'o’i tare da jagorancin Babban Limamin Ijebu.

Shugabanni da dama ciki har da Aliko Dangote, Yemi Osinbajo da Gwamna Dapo Abiodun sun yaba da jajircewar marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.