Bidiyon Pantami Ya Ziyarci Matar da Ta Reni Buhari Yana Jariri, Ta ba Shi Babbar Kyauta

Bidiyon Pantami Ya Ziyarci Matar da Ta Reni Buhari Yana Jariri, Ta ba Shi Babbar Kyauta

  • Tsohon Minista a Najeriya, Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyya ga wata dattijuwa da aka ce ita ta reni marigayi Muhammadu Buhari
  • Pantami ya ziyarci Mama Zainab da ake hasashen ta kai shekara 104 da haihuwa, wadda ta raini Buhari tun yana jariri
  • Tsohon minista ya tuna irin soyayyar da Buhari ke nuna wa Mama Zainab, yana cewa ya taba kai ta Abuja ta zauna tare da shi na wani lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Ana cigaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a garin Daura da ke jihar Katsina.

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Mama Zainab, tsohuwa mai shekara 104 da haihuwa.

Pantami ya ziyarci wacce ta reni Buhari
Pantami ya zayarci tsohuwa da ta riƙe Buhari yana jariri. Hoto: @ProfIsaPantami.
Source: Twitter

Pantami ya ziyarci wacce ta reni Buhari

Kara karanta wannan

'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients

Farfesa Pantami ya wallafa wani faifan bidiyon ziyarar da ya kai wa dattijuwar domin yi mata ta'aziyya a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isa Ali wanda ya kasance mai kaunar Buhari, ya bayyana ziyarar da ya kai mata a ranar Juma’a, 18 ga Yulin 2025.

Tsohon ministan ya ce ya ziyarci tsohuwar domin mata ta'aziyya a matsayin wacce ta raini Buhari tun yana jariri.

Kafin rasuwarsa, Buhari ya kai ta Abuja

Farfesa Pantami ya ce Mama Zainab ita ce ta kula da Buhari lokacin yana jariri wanda yake yawan yabonta kafin rasuwarsa.

A rubutunsa, Pantami ya bayyana Mama Zainab, wadda ake kiranta Tamadina, a matsayin uwa gare shi tun lokacin haihuwa.

Ya ce:

“Ta kasance kamar uwa ga Baba Buhari, shekaru da suka wuce, ya kawo ta Abuja ta zauna tare da shi."
Wacce ta reni Buhari ta ba Farfesa Pantami kyauta
Farfesa Pantami ya yi ta'aziyya ga dattijuwa da ta reni Buhari. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Yadda Buhari ke yabon dattijuwar kafin rasuwarsa

Pantami ya ce Buhari kansa ne ya faɗa masa labarin yadda Mama Zainab ta raine shi da irin kulawar da ta ba shi.

A yayin ziyarar, Mama Zainab da ake kira Tamadina ta tuna halayen Buhari, tana yabawa da gaskiyarsa da kamalarsa tun yana ƙarami.

Kara karanta wannan

Akpabio ya isa Daura don ta'aziyyar Buhari, ya fadi dabi'un tsohon shugaban

Pantami ya ƙara da cewa tsohuwar ta nace sai da ta ba shi kyauta, wato Alƙur’ani mai tsarki da darduma ta salla.

“Ta ce tun shekarunsa na ƙasa da 10, mutum ne mai gaskiya, mutunci, biyayya da ɗabi’a mai kyau tun ƙuruciyarsa."
“Ta nace sai na karɓi kyauta daga gare ta na Alkur'ani da darduma, Allah ya saka mata da alheri kuma ya jikan Baba Buhari da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya."

- Inji Pantami

Pantami ya tuna manyan kyaututtukan Buhari

Kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya ce ya zauna da Muhammadu Buhari na tsawon shekaru 24 kuma bai taba ganin rashin gaskiya a tare da shi ba.

Pantami ya bayyana cewa Buhari mutum ne mai gaskiya, kishin kasa da jajircewa, yana tunawa da kyawawan halayensa da sadaukarwa ga jama'a.

Tsohon ministan ya ce maganar cewa Buhari bai kyauta ba gaskiya ba ne, ya sha samun kyauta daga gare shi har guda biyu da ba zai manta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.